Guardiola ya kara shiga matsala a wasannin da yake fuskanta

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Manchester United a wasan mako na 16 a Premier League ranar Lahadi a Emirates.

City ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Josko Gvardiol tun kan hutu, kuma haka suka je hutu suka koma zagaye na biyu ƙungiyar Etihad tana cin 1-0.

Sauran minti biyu a tashi daga wasan na hamayya ne, United ta farke ta hannun Bruno Fernandes, sannan Ahmad Diallo ya kara na biyu daf da za a tashi daga karawar.

Kenan City ta yi nasara ɗaya daga karawa 11 a dukkan fafatawa, wadda aka doke karo na takwas da canjaras biyu daga ciki.

Haka kuma ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama, an zura mata ƙwallo biyu a raga a karawa ta takwas daga wasa 12 a lik, fiye da yawan da suka shiga ragarta a wasa 62.

City ta haɗa maki huɗu daga fafatawa bakwai a Premier League, rashin ƙwazo mai muni da ta yi tare da Southampton a kakar nan.

Maki 27 da City take da shi bayan wasannin mako na 16, shi ne rashin kokari a irin wannan matakin tun bayan 2010.

Manchester United ce kaɗai da take da maki 27 bayan mako na 15 ta je ta lashe Premier League a kakar 2002/03.

Harry Maguire ya buga wa United wasan, kuma karo na 250 da ya yi a Premier League, wanda ya ci ƙwallo 13 ya kuma bayar da 10 aka zura a raga

Da wannan sakamakon City tana nan a mataki na biyar a teburin Premier da maki 27, ita kuwa United mai maki 22 ta yi sama zuwa mataki na 13 a gasar.