Liverpool ta kara jefa Guardiola cikin ƙaƙa-ni-ka-yi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta doke Manchester City 2-0 a wasan mako na 13 a Premier League da suka kara a Anfield ranar Lahadi.

Cody Gakpo ne ya fara cin na farko a minti na 12, bayan da Mohamed Salah ya tura masa ƙwallon.

Kenan karo na 36 da Salah ya zura ƙwallo a raga ko ya bayar aka ci a Premier League, wanda ya yi kan-kan-kan da Wayne Rooney a irin wannan bajintar.

Daga baya Salah ya kara na biyu a bugun fenariti, kuma 99 a Anfield a Premier, saura ɗaya ya shiga cikin ƴan takwas da suka ci 100 a wasannin gida.

Haka kuma Salah ya ci City ƙwallo na 12 a dukkan fafatawa, shi ne kan gaba a yawan zura mata ƙwallaye a raga a tarihi.

Wannan shi ne karo na bakwai a jere da Pep Guardiola ya ja ragama a dukkan fafatawa ba tare da nasara ba da canjaras a ɗaya daga ciki.

A wasan na hamayya an zufe City, wadda sai a minti na 39 ta buga ƙwallon da ya nufi ragar Liverpool, karon farko da ta kasa yin abin kirki tun bayan Afirilun 2010 a wasa da Arsenal.

Wannan shi ne karon farko a Premier League tsakanin Liverpool da City da suka kara ba tare da mai tsaron raga Alisson ko Ederson ba, tun bayan Maris ɗin 2017.

Da wannan sakamakon Liverpool ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburi da tazarar maki 11 tsakaninta da City mai rike da kofin bara.

Arsenal ce ta biyu da maki 25, iri ɗaya da na Chelsea ta uku, wadda ta doke Aston Villa 3-0 ranar Lahadi a Stamford Bridge.