Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na matuƙar son ɗaukar Anderson, Arsenal na harin Etta Eyong
Elliot Anderson na cikin ƴan wasan da Machester Unite ke fatan ɗauka, Arsenal na harin dan wasan gaban Kamaru Etta Eyong daga Levante, Ivan Toney ba zai koma Saudiya a watan Janeru.
Manchester United za ta ɗauki ɗan wasan tsakiyar Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, 23, a kakar siyen yan wasa a Janeru. (Mirror)
Ɗan wasan gaban Levante's da Kamaru Etta Eyong, 22, da ƙungiyoyi masu yawa ke son ɗauka, Arsenla ce kan gaba wajen harin daukar ta sa. (Sport - in Spanish)
Ɗan wasan gaba na Ingila Ivan Toney, 29, ba zai tafi Al-Ahli a watan Janeru ba, a cewar daraktan wasannin Saudiya Rui Pedro Braz. (Goal)
A kakar wasanin na mai zuwa kwantaragin ɗan wasan gaban Poland Robert Lewandowski za ta ƙare, inda Barcelona, ta ce nan gaban zai yanke makomar sa. (Footmercato - in French)
Tottenham na son ɗaukar Takefusa Kubo mai shekaru 24, a watan Janeru daga are interested in a move for Japan winger Takefusa Kubo, 24, daga Real Sociedad. (Football Insider)
Spurs na duba yiwuwar ɗaukar Maghnes Akliouche, mai shekaru 23, yayin da suke shirye shiryen tattaunawa da Monaco. (TeamTalk)
Wolves na son daukar aron mai tsaron ragar Lazio Christos Mandas, mai shekaru 24. (Il Messaggero - in Italian)
Ɗan wasann Crystal Palace Daniel Munoz mai shekaru 29, ya ce yan burin ganin fatan sa na taka leda a Manchester United mafarki ne da zai iya tabbata. (AS - in Spanish)
Pep Guardiola ya bayana takaicinsa kan yadda Claudio Echeverri, da Manchester City ta bayar da aronsa ga Bayer Leverkusen, baya samun damar buga wasa yadda ya kamata. (Bild - in German)
West Ham na kan bakanta na siyar da ɗan wasan gaban Jamus Niclas Fullkrug, 31, a kakar cinikin ƴan wasa. (Football Insider)
Chelsea ta amince da tayin ɗauko Deinner Ordonez, mai shekaru 16, daga Independente del Valle, inda zai koma ƙungiyar a 2028, idan ya cika shekaru 18.. (Fabrizio Romano)
Bayern Munich da Borussia Dortmund na rige -rigen ɗaukar Nathan de Cat, mai shekaru 7, daga Anderlecht. (Sky Sports)