Man City ta dage kan Enzo Fernandez, Arsenal na zawarcin Barcola

Enzo Fernandez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City na duba yadda za ta ɗauke ɗanwasan tsakiyar Argentina da Chelsea mai shekara 25, Enzo Fernandez, yayin da ɗanwasan tsakiyar ƙungiyar da Sifaniya mai shekara 30, Rodri, ke sa ran komawa Barcelona. (Independent)

Arsenal za ta yi gogayya da Manchester United kan ɗanwasan gaban Italiya mai shekara 21, Pio Esposito, wanda Inter Milan ta sanya wa farashin £73m. (Sun)

Liverpool ta tattauna da Paris St-Germain kan ɗanwasan gaban Faransa, Bradley Barcola, amma babu wani ƙari da ƙungiyar ta yi kan farashin da ta fara sanya wa ɗanwasan mai shekara 23. (Sky Sports)

Bayan gaza ɗaukar ɗanwasan gaban Brazil mai shekara 26, Vinicius Jr daga Real Madrid, Arsenal ta karkata kan Barcola, da ɗanwasan gaban Atletico Madrid da Argentina mai shekara 26, Julian Alvarez da kuma ɗanwasan gefen Everton da Senegal mai shekara 26, Iliman Ndiaye, 26. (Independent)

Newcastle ta shaidawa Manchester United cewa ba za ta sayar da ɗanwasan bayan ta, Lewis Halla ba, bayan ƙin amincewa da tayin farko kan ɗanwasan Ingilan mai shekara 21. (Sky Sports)

Abokan taka ledar Ezri Konsa a Aston Villa sun yarda cewa ɗanwasan bayan Ingilan mai shekara 28 zai bar su domin komawa Arsenal. (Mail - subscription required)

Arsenal na ƙoƙarin ɗauke Cristian Romero, amma Tottenham ba ta da niyyar sallama ɗanwasan bayan Argentina mai shekara 28 ga abokiyar hamayyarta ta arewacin London. (Mirror)

Newcastle na bibiyar ɗanwasan tsakiyar Marseille da Denmark mai shekara 31, Pierre-Emile Hojbjerg. (Mail)

Napoli na ƙoƙarin ɗaukar ɗanwasan bayan Chelsea da Faransa mai shekara 25, Benoit Badiashile, a matsayin aro. (Sky Sports)

Napoli ta karkata ga neman ɗanwasan gaban Arsenal da Brazil mai shekara 29, Gabriel Jesus, 29. (Calciomercato - in Italian)

Kocin Newcastle, Matthias Jaissle zai yanke hukunci kan makomar Jacob Murphy, inda rahotanni ke cewa Everton na zawarcin ɗanwasan gefen Ingilan mai shekara 31. (Football Insider)