Real ta kafa tarihin zama ta farko da ta samu sama da yuro biliyan 1

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Real Madrid ta zama kungiyar kwallon kafa ta farko a duniya da ta kafa tarihin samun kudi sama da yuro miliyan dubu daya (biliyan daya) a shekara kamar yadda sharhin kamfanin haraji na Deloitte da ke Landan ya bayyana.

Nazarin kamfanin na Deloitte ya nuna cewa kungiyar ta Sifaniya ta ci gaba da zama ta daya a jerin kungiyoyin da ke gasa daban-daban ta kwallon kafa a duniya inda kudin da ta samu ya kai yuro biliyan 1.05 kwatankwaci fam miliyan 883 daga kakar da ta wuce ta 2023-24, lokacin da ta dauki kofin La Liga da kuma na Zakarun Turai (Champions League).

Harwayau kuma nazarin ya nuna cewa Manchester City ita ma ta sake zama ta biyu a jerin kungiyoyin da suka fi samun kudi inda take da fam miliyan 708.

Zakarun na Premier sun dauki kofin gasar ta Ingila sau hudu a jere da kofin duniya na kungiyoyi da kuma kofin zakaran zakaru na Turai (European Super Cup), a kakar da ta gaba.

Manyan kungiyoyi biyar da ke bin baya su ne Paris St-Germain, wadda ta samu fam miliyan 681, sai Manchester United mai fam miliyan 651, da kuma Bayern Munich wadda ta samu fam miliyan 646.

A karon farko kuma Aston Villa ta zama cikin kungiyoyi 20 na jerin farko da suka fi samun kudi bayan da ta yi nasarar shiga gasar Zakarun Turai, tun 2011.

Kungiyoyin gasar Premier tara ne suka kasance cikin jerin 20 da ke gaba-gaba wajen samun kudin inda Arsenal, da Liverpool, da Tottenham, da Chelsea, da Newcastle da kuma West Ham suka ci gaba da rike matsayinsu.

Jerin Kungiyoyi 10 na farko a teburin Deloitte na 2025 da kudin da suka samu

Matsayi Kungiya Tikitin wasa Nunawa a kafar Labarai Talla Jumulla

( Bara )

1 (1) Real Madrid 248,000 316,000 482,000 1,046,000

2 (2) Man City 88,000 343,000 407,000 838,000

3 (3) PSG 170,000 245,000 391,000 806,000

4 (5) Man Utd 152,000 258,000 360,000 771,000

5 (6) Bayern Munich 131,000 213,000 421,000 765,000

6 (4) Barcelona 103,000 236,000 421,000 760,000

7 (10) Arsenal 153,000 305,000 258,000 717,000

8 (7) Liverpool 132,000 240,000 343,000 715,000

9 (8) Tottenham 123,000 195,000 297,000 615,000

10(9) Chelsea 93,000 190,000 262,000 546,000