Al-Hilal ta sake taya Osimhen, Real Madrid na harin Konate

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Al-Hilal ta ƙasar Saudiyya ta inganta tayin da ta gabatar kan ɗan wasan gaba na Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 26, inda ta ke shirin biyan sa albashin fam miliyan 42.6m duk shekara. (Goal)

Real Madrid na fatan ɗaukar ɗan wasan bayan Liverpool Ibrahima Konate, mai shekara 26, kan cinikin kyauta a bazara mai zuwa, lokacin da kwantiragin ɗan ƙasar Faransan zai ƙare. (Marca)

Arsenal na zawarcin ɗan wasan gaba na Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, da kuma ɗan wasan RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22, duk da cewa ɗan wasan gaba guɗa ɗaya kawai ta ke niyyar ɗaukowa a wannan bazarar. (Mirror)

A wani ɓangare kuma, Arsenal ɗin na ganin farashin Gyokeres ya yi tsada don haka za ta mayar da hankali kan ɗaukar Sesko ko kuma ɗan wasan Aston Villa da Ingila Ollie Watkins, mai shekara 29. (Record)

Ɗan wasan gaba na Manchester United Rasmus Hojlund, mai shekara 22, ya bayyana a matsayin ɗan wasan da ke kan gaba a jerin sunayen ƴanwasan da Inter Milan ke hari a wannan bazarar. (Gazzetta dello Sport)

Ƙungiyar ta Old Trafford ta yanke shawarar ci gaba da riƙe ɗan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24. (Corriere dello Sport).

AC Milan ta fara tattaunawa da Arsenal kan cinikin ɗan wasan bayan Gunners Oleksandr Zinchenko, mai shekara 28. (Corriere dello Sport)

Manchester United ta tuntuɓi wakilan ɗan wasan gaban Faransa Hugo Ekitike, mai shekara 22, wanda ke taka leda a Eintracht Frankfurt (Bild),

Chelsea da Aston Villa da Tottenham duk suna sha'awarsu kan ɗan wasan gaban Manchester United Alejandro Garnacho, mai shekara 20, bayan da aka shaida wa ɗan wasan ƙasar Argentina cewa ya nemi sabon kulob. (Mail)

Galatasaray ta gabatar da tayi kan golan Barcelona Marc-Andre ter Stegen mai shekara 33. (Sport)

FC Porto ta nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gefe na Southamton Tyler Dibling, mai shekara 19 (Record)

Ƙungiyoyin Serie A da na Premier League ɗin Ingila sun tuntuɓi Bayer Leverkusen kan batun yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba Patrik Schick mai shekara 29 (Sky Germany)