Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Ukraine ke fafutikar gyara lantarkinta da hare-haren Rasha suka lalata
- Marubuci, Paul Adams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent
- Aiko rahoto daga, Ukraine
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da lokacin hunturu ke karatowa a Ukraine, abubuwa na ta faruwa.
Injiniyoyi na can sun dukufa wajen aikin gyara layukan lantarki da aka lalata a wani hari da Rasha ta kai kan cibiyar makamashin Ukraine ɗin.
Saboda dalilai na tsaro, ba a ba mu damar faɗan wurin da muke ba ko kuma lokacin da muka kai ziyara. Kuma ba za mu iya kwatanta girman ɓarnar da harin ya yi ba, ko cewa cibiyar lantarkin na ci gaba da aiki.
Rasha, kamar yadda aka faɗa mana, na karɓar bayanai ta ko'ina domin amfani da su wajen sanin inda za ta ƙara kai hari.
A ranar Alhamis, Moscow ta kai wani hari mai munin gaske kan cibiyar makamashin Ukraine a cikin ƙasa da mako biyu.
Irin waɗannan hare-hare, sun janyo nakasu ga ɗaukacin ɓangaren lantarkin Ukraine a wannan shekara.
Kafin hari na farko a wannan wata, ranar 17 ga watan Nuwamba, Ukraine ta riga ta rasa megawatt 9 na karfin wuta. Hakan ya kai rabin wutar da aka samu a bara.
An buƙaci cewa kada mu bayyana cewa cibiyar makamashi da muka ziyarta na cikin waɗanda aka kai wa hari ranar Alhamis.
Sai dai kamar saura a faɗin ƙasar, wannan daɗaɗɗen cibiyar lantarki ta sha fuskantar hare-haren jirage mara matuki da kuma na linzami tun bayan da shugaba Vladimir Putin ya kaddamar da mamaya kan Ukraine a watan Febrairun 2022.
Akwai tasirin hare-haren Rasha a ko'ina.
A wani lungu na cibiyar, ma'aikata ne ke aikin gyara wurare da aka lalata.
An samar da abubuwa kamar robobi kan na'urorin cibiyar domin kare shi daga wasu hare-haren.
"Lamarin mai muni ne," in ji Oleksandr. Mun amince ba za mu bayyana asalinsa ba.
"Ba mu da ko lokacin sake gyara manyan na'urori da ke samar da lantarki, balle mu kai ga saman cibiyar da kuma bangonsa. An sake lalata komai daga wannan hari zuwa wancan."
Ƙawayen Ukraine na ƙasashen yamma na ƙokarin taimakawa.
A ranar Litinin, kamfanin makamashi mai zaman kansa mafi girma a Ukraine (DTEK), ya ce ya samu dala miliyan 113 daga Tarayyar Turai da kuma gwamnatin Amurka domin ya taimaka wajen sake gyara na'urorin bayar da lantarki da kuma kare su daga dutsar kankara, da ruwan sama da kuma yanayi.
Sai dai mutanen da aka ɗora wa alhakin sake mayar da lantarkin Ukraine, na da babban aiki a gabansu.
A cikin wani ɗaki, wanda aka saka wasu abubuwa domin kare shi daga hari, Dmytro ne yake ciki yana hutawa.
"Wasu suna kare ƙasa a fagen daga," in ji shi. "Mu kuma muna nan muna kare makamamashin mu."
Amma yayin da injiniyoyi daga DTEK ke ƙokawa da irin aiki da ke gabansu da kuma zama cikin shirin ko ta-kwana kan ci gaba da kai hare-hare da Rasha ke yi, sauran ƙasar na yin abin da take yi tun lokacin da aka fara yaƙin: sabawa da rayuwa cikin yaƙi.
A daidai lokacin da ake shirin shiga sanyi, titunan birane sun sake cika da hayaniya da kuma ruri na sautin injunan bayar da hasken wuta. Watakila za a kashe fitulun kan titi, amma hasken da ke shaguna da gidajen cin abinci na ci gaba da haskakawa.
Turirin man dizal ya mamaye sanyin iskar da ke kaɗawa.
A cikin wuraren hasumiya, inda yanke wutar lantarki ke hana ruwan zafi isa saman benaye, mazauna yankin da suka riga suka fara amfani da nau'rorin cajin waya da kuma toshila , tuni suka fara ƙirƙira.
Wasu sun saka batura da kuma na'urorin bayar da hasken wuta cikin gidajensu, wanda ke fara aiki da zarar an ɗauke lantarki.
A cikin wani katafaren gida mai bene 25 a unguwar Pozniaky na Kyiv, gida mai ɗauke da mutane kusan 700, mazauna wurin sun haɗa kai don kafa wani babban injin amar da hasken wuta, wanda zai iya saka ruwan zafi haura wa zuwa benaye na sama.
Ga Nataliya Andriyko, wadda ke zaune a hawa na 19 tare da mijinta da dabbobin gida, abin farin ciki ne.
"Abin ban mamaki ne," ta faɗa min yayin da muke zaune a cikin ɗakin dafa abinci wanda wata fitila ɗaya mai amfani da batir ta haska.
“Abin ban tsoro ne yadda nake farin cikin samun waɗannan buƙatu na yau da kullum. Hakan na nufin yanzu zan iya saukar da kare a ƙasa a cikin na'urar ɗaukar mutane maimakon matakala a cikin duhu. Ga shi kuma ina da ruwa a cikin famfo."
Bayan lokacin hunturu guda biyu masu wuya, Nataliya ta yaba wa waɗanda suke zaune tare.
"Muna da mutane masu karamci," in ji ta. "Mutanen da suka san zamani, waɗanda suke da yakinin cewa za a iya kirkirar abu."
"Idan muka haɗa kai, za mu zama masu karfi."
Matsalar ɗaukewar lantarki abu ne da mutane ke fama da shi a faɗin ƙasar, inda mutane ke duba wayoyinsu domin sanin yaushe za a sake ɗauke wuta, da kuma fitar da kuɗi domin sayen injunan samar da hasken wuta da kuma makamashin samun wutar lantarki ta hanyar hasken rana.
Ga waɗanda suka shirya fim ɗin "Zbory OSBB", abun mamaki ne batun rashin wutar.
Fim ɗin wanda za a haska a farkon watan Disamba, ya nuna wasu mutane na ribibin sayen injunan janareto, yayin da aka tinkari lokacin hunturu.
"Idan kana da mutum sama da 10 kuma suna son cimma matsaya ɗaya, abin yana yawan kasancewa da barkwanci," in ji furodusan fim ɗin kuma marubucin labarin, Ivan Melashenko.
Ya ce ya samu bayanai na fara rubuta labarin fim ɗin ne a wani zauren dandalin whatsapp na makwabtansa.
"Abin kamar mafarki ne, saboda kowaye na da nasa ra'ayi kuma da wuya a samu mafita," in ji Ivan.