Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Palmer ya kafa tarihin cin fenariti ba tare da ɓararwa ba
Ranar Lahadi Chelsea ta je ta doke Tottenham 4-3 a wasan mako na 15 a Premier League.
Cole Palmer ne ya ci wa Chelsea biyu daga ciki a bugun fenariti, kenan na 12 jimilla ba tare da ya ɓarar da ko ɗaya ba, shi ne kan gaba a wannan bajintar a Premier.
Tsohon ɗan wasan Manchester City, Yaya Toure shi yake rike da bajintar a baya mai 11 a raga ba tare da ya zubar da ko ɗaya ba.
Ivan Toney ya kasa cin ɗaya, bayan da ya zura 10 a raga a bugun daga kai sai mai tsaron raga a Brentford, inda Nick Pope na Newcastle ya tare wanda ya buga na 11.
Dimitar Berbatov ya zura dukkan taran da ya buga a raga a bugun fenariti a Premier, ɗan wasan Fulham, Raul Jimenez ya ci takwas daga takwas da ya yi.
Shima Bryan Mbeumo ya ci fenatiti takwas daga takwas da ya yi da kuma Chriss Wood na Nottingham Forest mai bakwai a raga daga fenariti bakwai.
Tsohon ɗan wasan Southampton, Matt Le Tissier ya zura 25 a raga daga 26 a fenariti a Premier League.
Danny Murphy da Callum Wilson da James Beattie da Julian Dicks da Erling Haaland kowanne ya ci fenariti 15 da kasa cin ɗaya.
Palmer ba shi ne ya fara cin ƙwallo biyu ba a bugun daga kai sai mai tsaron raga ba a bana, domin ɗan wasan Bournemouth, Justin Kluivert ne ya fara bajintar.
Bournmouth ta yi nasara a kan Wolverhampton da cin 4-2 a Premier League, inda Kluivert ya zura uku rigis a raga daga ciki a bugun fenariti.
Alan Shearer ne ke rike da yawan cin fenariti a tarihin Premier League mai 56, idan ka cire waɗanda ya kasa ci, sai Frank Lampard da tazarar 13 tsakani da na Shearer.