Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasa nawa Real Madrid za ta yi kafin gasar kofin duniya?
Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 32, bayan wasa 12 a gasar La Liga ta bana.
Haka kuma ita ce kan gaba a rukuni na shida a teburin Champions League mai maki 10, bayan buga wasa biyar.
Ranar Lahadi Real ta tashi wasa 1-1 a gida da Girona, karo na biyu da ta buga kunnen doke, bayan wanda ta yi da Osasuna a bana cikin watan Oktoba.
Ranar Asabar Barcelona ta je ta doke Valencia 1-0 ta karbi teburin da maki 31, daga baya Real ta koma matakin, bayan raba maki da Girona.
Wasa uku ya rage a gaban Real Madrid daga nan a fara gasar kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci a bana.
Real Madrid wadda ta kai zagayen gaba a Champions League za ta buga wasan karshe a cikin rukuni ranar 2 ga watan Nuwamba da Celtic a Santiago Bernabeu.
Kwana biyar tsakani Real za ta ziyarci Real Vallacano domin karawa a wasan mako na 13 a gasar La Liga, wato ranar 7 ga watan Nuwamba.
Wasa na karshe da Real za ta yi sai gasar kofin duniya, shi ne da Cadiz a gida ranar 10 ga watan Nuwamba a fafatawar mako na 14.
Za a fara wasannin gasar kofin duniya ranar 20 ga watan Nuwamba a karkare ranar 18 ga watan Disama.
A karon farko tawagogi 32 ne za su kece raini a filaye takwas a Qatar.
Ga jerin wasan da suka ragewa Real Madrid kafin gasar kofin duniya:
Champions League Laraba 2 ga watan Nuwamba
- Real Madrid da Celtic
Spanish La Liga Litinin 7 ga watan Nuwamba
- Real Vallecano da Real Madrid
Spanish La Liga Alhamis 10 ga watan Nuwamba.
- Real Madrid da Cadiz
Da zarar an gama gasar kofin duniya za a ci gaba da wasannin La Liga, inda Real Madrid za ta ziyarci Valladolid ranar 31 ga watan Disamba.
Real Madrid ce ke rike da Champions League na 14 jumulla, ita ce ke rike da La Liga da ta lashe a bara.