Newcastle na son Larsen, Wilson ya daidaita da West Ham

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United ta kwaɗaitu da ɗan wasan Wolves' mai shekara 25 daga Norway, Jorgen Strand Larsen wanda ake son ya maye gurbin ɗan wasan Sweden, Alexander Isak mai shekara 25. (Express & Star, external)
Ɗan wasan Ingila mai shekara 39, Callum Wilson ya amince da yarjejeniyar da aka gabatar masa daga West Ham bayan baro Newcastle a watan da ya gabata. (Talksport, external)
Manchester City ta gabatar da sabon tayi kan ɗan wasan Newcastle, Tino Livramento kuma a shirye take ta biya sama da fam miliyan 50 kan ɗan wasan na Ingila. (TBR Football, external)
Bayern Munich ta koma teburin tattaunawa da Liverpool kan Luis Diaz amma ƙungiyar ta Bundesliga ba ta gabatar da tayinta ba a karo na biyu kan ɗan wasan mai shekara 28. (Athletic - subscription required, external)
Manyan ƙungiyoyin firimiyar Saudiyya biyu sun nuna zawarcinsu kan Antony da ke taka leda a Manchester United bayan kammala zaman aro a Real Betis. (Sky Sports, external)
Ɗan wasan Ingila Luke Shaw zai saurari tayin da ƙungiyoyin Saudiyya suka gabatar, yayinda ɗan wasan mai shekara 30 ke shirin barin Manchester United bayan kaka 11 a Old Trafford. (Sun, external)
Manchester United ba tayi nasara ba a neman aron ɗan wasan Aston Villa da Argentina mai tsaron raga, Emiliano Martinez mai shekara 32. (Sun)
Chelsea ta sha mamaki bayan watsi da tayin da ta gabatar kan ɗan wasan gaba a Juventus mai shekara 20 daga Turkiyya, Kenan Yildiz. (La Gazzetta dello Sport - in Italian, external)
Fulham na gab da kammala yarjejeniya da ɗan wasan mai tsaron raga daga Faransa, Benjamin Lecomte, mai shekar4a 34 da ke Montpellier. (Standard)
Everton na bibiyar ɗan wasan Southampton mai shekara 19, Tyler Dibling. (Times - subscription required, external)
Leeds United ta gabatar da tayin £26m kan ɗan wasan Feyenoord, Igor Paixao, sai dai ita ma Roma ta bi sahun Marseille a fafutikar ɗan wasan na Brazil mai shekara 25. (Sky Sports, external)










