Ko Barcelona za ta amfana da damar da ta samu a La Liga?

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona za ta karɓi bakuncin Rayo Vallecano a gasar La Liga da za su fafata ranar Litinin, kuma da zarar ta ci wasan za ta koma ta ɗayan teburi.

Barcelona tana mataki na uku a teburin La Liga da maki 58 da tazarar maki uku tsakani da Real Madrid ta ɗaya, ita kuwa Rayo mai maki 35 tana ta shidan teburi.

Ƙungiyoyin biyu sun kara a bana ranar Talata 27 ga watan Agustan 2024, inda Barcelona ta je ta ci Vallecano 2-1 a gasar ta La Liga.

Barcelona aka fara ci a ranar ta hannun Unai Lopez a minti tara da take leda daga baya ta farke a zagaye na biyu ta hannun Pedri da Dani Olmo.

Daga Oktoban 2021, Barcelona ta yi wasa 14 a jere tana doke Rayo har da cin 7-0 da 6-0 da kuma 6-1.

Daga nan kuma Barcelona ta yi karawa biyar ba tare da cin Rayo ba daga ciki aka doke ta uku a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

A kakar bara sun tashi 1-1 a gidan Rayo cikin Nuwambar 2023, sannan Barcelona ta yi nasarar zura 3-0 a wasa na biyu a La Liga cikin watan Mayun 2024.

Sakamakon wasa biyar baya tsakanin Rayo Vallecano da Barcelona a La Liga:

Ranar 27 ga watan Agustan 2024

  • Rayo Vallecano 1-2 Barça

Ranar 19 ga watan Mayun 2024

  • Barça 3-0 Rayo Vallecano

Ranar 25 ga watan Nuwambar 2023

  • Rayo Vallecano 1-1 Barça

Ranar 26 ga watan Afirilun 2023

  • Rayo Vallecano 2-1 Barça

Ranar 13 ga watan Agustan 2022

  • Barça 0-0 Rayo Vallecano