Man City za ta fuskanci Real Madrid da ƙwarin gwiwa

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta kai zagayen gaba a FA Cup, bayan da ta je ta doke Leyton Orient da ci 2-1 ranar Asabar.
Tun a minti na 16 da fara wasa ne City ta ci gida ta hannun mai tsaron raga, Orgeta, sakamakon wata ƙwallo mai kayatarwa da Jamie Donley ya buga masa daga nesa.
Haka suka je hutu ana cin City, mai rike da kofin Premier League 1-0, sai da suka koma zagaye na biyu ne ta samu ta farke ƙwallayen.
City ta fara zare ɗaya ta hannun sabon ɗan wasan da ta ɗauka a Janairu, Abdoukodir Khusanov a karawar da mai buga League One.
Saura minti 12 a tashi daga wasan ne Kevin de Bruyne ya kara na biyu a raga, wanda ya shiga fafatawar daga baya.
Rabonda wata karamarr ƙungiya ta yi waje da City a FA Cup tun bayan 2018.
Wannan sakamakon zai karawa ƙungiyar Etihad ƙwarin gwiwa a shirin karawar da za ta karɓi bakuncin Real Madrid a Etihad a makon gobe.
Ranar Talata 11 ga watan Fabrairu, Real Madrid za ta je City, domin buga wasan cike gurbi a Champions League na kakar nana.
Real mai rike da kofin zakarun Turai za ta buga karawar cike gurbi ne, sakamakon da ta kare a mataki na 11 a kan teburi, bayan wasa takwas a cikin rukuni.
Ita kuwa City mai rike da Premier League ta kammala ne a matsayi na 22 a teburin Champions League.
To sai dai Real Madrid, wadda za ta fafata da Atletico Madrid ranar Asabar a La Liga tana matakin farko a kan teburi da maki 49.
Ita kuwa City, wadda ke fuskantar kalubale a kakar nan, tana mataki na biyar a teburin Premier League da maki 41.
Cikin wasa 24 da City ta kara a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan ta ci wasa 12 da canjaras biyar aka doke ta karo bakwai da cin ƙwallo 48 aka zura mata 35 a raga.












