Lookman yana cikin ƴan takara biyar a gwarzon Afirka na bana

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Najeriya, Ademola Lookman yana gaba a jerin ƴan takara biyar a ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon kafar Afirka na bana.

Hukumar ƙwallon kafar Afirka, Caf ce ta bayyana sunayen ƴan wasan ranar Litinin da ake sa ran fayyace gwarzon bana.

Lookman ya ci ƙwallo uku a wasan karshe a Europa League da ta kai Atalanta ta lashe kofin, sannan ya taka rawar gani da Super Eagles ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a yi a baɗi.

Yana takara tare da ɗan kasar Morocco, Achraf Hakimi, wanda ya lashe Ligue 1 a Paris St Germain da ɗan kasar Guinea, Serhou Guirassy, wanda ya ci ƙwallo 28 a Bundesliga a kakar da ta wuce a Stuttgard, hakan ya sa Borussia Dortmund ta saye shi.

Sauran sun haɗa da Simon Adinga mai taka leda a Brighton & Hove Albion, wanda ya buga gasar da Ivory Coast ta lashe kofin Afirka da mai tsaron ragar Afirka ta Kudu, Ronwen Williams.

Kociyoyin tawaga 54, waɗanda suke mamba a hukumar ƙwallon kafar Afirka ke yin zaben tare da wasu ƙwararrun.

Ana sa ran bayyana gwarzon ɗan ƙwallon kafar Afirka na bana ranar 16 ga watan Disamba a birnin Marrakech a Morocco.