Da wuya Rashford ya sake buga wa Man Utd, Arsenal na zawarcin Nico Williams

Asalin hoton, Getty Images
Ba lalle ba ne ɗanwasan Ingila Marcus Rashford, da ya bar Manchester United zuwa Aston Villa a matsayin aro, ya sake buga wa ƙungiyarsa ta asali saboda dangantakarsa da ƙungiyar. (Guardian).
Newcastle United na zawarcin ɗanwasan Bournemouth ɗanasalin Netherlands Justin Kuivert, 25 ko da yunƙurinta na sayen ɗanwasan Sweden Alexander Isak, 25, a bazara bai tabbata ba. (Sun).
Newcastle da Tottenham na iya farfaɗo da sha'awarsu ta son ɗaukan ɗanwasan Crystal Palace Marc Guehi, 24 a bazara idan ya shiga shekarar ƙarshe ta kwantiraginsa bayan da aka yi fatali da tayin Spurs a ƙarshen kasuwar musayar ƴanwasa ta watan Janairu. (Sky Sports).
Kocin Napoli Antonio Conte ya ji takaicin yadda ƙungiyarsa ta gaza sayen ɗanwasan Manchester United Alejandro Garnacho, 20, ko kuma ɗanwasan gaba na Jamus Karim Adeyemi, 23 daga Borussia Dortmund a Janairu bayan cefanar da ɗanwasa Khvicha Kvaratskhelia, 23, ga Paris St-Germain. (Sky Sports Italia, via Football Italia).
Manchester United da Bayern Munich sun yi rububin Christopher Nkunku a Janairu amma suka dakatar da sha'awarsu saboda farashin da Chelsea ta saka kan ɗanwasan mai shekara 27. (Mail).
Har yanzu ɗanwasan Athletic Bilbao Nico Williams na cikin ƴanwasan da kocin Arsenal Mikel Arteta ke son ɗaukowa. (Football Transfers).
Ɗanwasan Arsenal Jorginho, 33 ya sa hannu kan wata yarjejeniya ta koma wa Flamengo a bazara idan kwantiraginsa da Arsenal ya ƙare. (Mirror).
Carlisle United da ke ƙasan teburi a gasar League Two, na duba yiwuwar naɗa Steven Gerrard a matsayin sabon kocinta sakamakon barin Al-Ettifaq da tsohon kyaftin ɗin na Liverpool ya yi a baya-bayan nan. (Mail).












