Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alexander-Arnold na tare da Liverpool 100 bisa 100 - Slot
- Marubuci, Ben Collins
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 1
Kocin Liverpool Arne Slot ya haƙiƙance cewa "hankalin Trent Alexander-Arnold yana kanm" baki ɗaya yayin da ake ta raɗe-raɗi game da makomar ɗanwasan.
Kwantaragin ɗanwasan bayan na Ingila mai shiekara 26 zai ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana.
Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa Real Madrid ta fara tunkarar ɗanwasan amma dai ba ta miƙa wani tayi ba tukunna game da sayensa a watan nan na Janairu.
Kafofin yaɗa labarai a Sifaniya sun ruwaito cewa Real na da niyyar sayensa a watan nan, amma Slot ya ce yana da ƙwarin gwiwar ba za a janye hankalinsa ba, har ma ya tabbatar cewa yana cikin tawagarsa da za su kara da Manchester City a ƙarshen makon nan.
"Ina tabbatar zai buga wasan ranar Lahadi kuma muna fatan zai yi abin da ya saba yi," in ji Slot.
"Ina ganin kowa ya ga ƙoƙarinsa a rabin kakar nan, da yadda yake hanƙoron cin kofuna da nasara.
"Ina ganin yadda yake mayar da hankali a filin atasaye a kullum. Hankalinsa yana tare da mu kuma zai buga wasa ranar Lahadi."
Akwai raɗe-raɗi game da makomar Mohamed Salah da Virgil van Dijk yayin da su ma suka shiga wata shida na ƙarshen kwantaraginsu.