Fatawar Sheikh Jabir Maihula kan abu biyar da ba su karya azumi

Sheikh Dr Jabir Sani Maihula

Asalin hoton, Facebook/Jabir Sani Maihula

Bayanan hoto, Sheikh Dr Jabir Sani Maihula sanannen malami ne a arewacin Najeriya kuma babban malamin jami'a ne a jihar Sokoto
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Akwai sharuɗɗa da ladubba kan kowace ibada ta addinin Musulunci, cikinsu har da azumin Ramadana wanda ɗaya ne daga cikin rukunnan addinin.

Babban abin da mai azumi zai ƙaurace wa yayin azumi shi ne ci da sha tun kafin fitowar ranar har zuwa faɗuwarta, duk da cewa akwai sauran sharuɗɗa.

Sai dai akwai wasu abubuwa da wasu ke ganin suna karya wa mutum azumi alhalin kuma ba haka ba ne.

Sheikh Dr Jabir Maihula wanda malamin addinin Musulunci ne a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, ya lissafa wasu abubuwa biyar da jama'a da dama ke tunanin na karya azumi amma ya ce sam ba su karya azumin.

1) Fitar Maziyyi

Daga cikin abubuwan da jama'a ke tunanin suna karya ko kuma raunata azumi akwai fitar maziyyi.

A cewar malamin: "Maziyyi shi ne abin da ke fita daga gaban namiji ko mace saboda sha'awa ƙarama, ba lokacin jima'i ba.

"Wani zubin yakan fita daga jikin mutum ba tare da ya sani ba saboda yakan fita ne kaɗan-kaɗan. Akasari sha'awa ta kallon wani abu da ido ce ke haifar da shi.

"Bisa fatawa mafi inganci maziyyi ba ya karya azumi."

2) Amfani da man goge baki

Da dama dai masu azumi kan bar bakinsu ba tare da yin burushi ba saboda tsoron ka da su karya azumin nasu.

Wani lokacin kuma wasu masu azumin ba sa son yin amfani da man goge baki ne saboda ka da "warin bakin mai azumi" ya tafi su rasa ladan hakan.

To sai dai Sheikh Maihula ya ce "duk malaman wannan zamani, kamar bin Uthaimin, da bin Baz, da kwamatocin masu fatawa na duniya sun ce amfani da man goge baki ba shi karya azumi."

Malamin ya ci gaba da cewa "saboda ba abin ci ba ne, ba abin sha ba ne, kuma ba shi kaiwa ciki - sai dai fa idan mutum haɗiyewa ya yi da gangan."

3) Ɗaukar jini ko allura

Sai dai Sheikh Jabir ya ce baya ga amfani da man goge baki, akwai wasu abubuwa da suka jiɓanci lafiyar ɗan'adam da ba su karya azumin idan aka yi su.

"Misali shi ne ɗaukar jinin mutum idan ba shi da lafiya domin a yi gwaji. Wannan ba shi karya azumi."

Malam ya ƙara da cewa: "Muna dai bayar da shawarar kada mutum ya ce zai bayar da jini domin a ƙara wa wani, saboda akwai saɓani na malamai mai ƙarfi a kan hakan saboda yawan jinin da mutum zai bayar."

Haka nan, yi wa mutum allura ba shi karya azumi, amma da sharaɗi. "Amma kada allurar ta zama ta madadin abinci ce. Misali, akwai mutanen da ba su iya cin abinci ko abin sha, sai a dinga yi musu allura a madadin haka."

4) Maganin shaƙa na asma

Kazalika, malam ya ce amfani da maganin da masu cutar asma ke shaƙa mai suna inhealer a Turance ba shi karya azumi.

"Saboda ba abinci ba ne, ba abin sha ba ne, kuma ba shi kaiwa cikin mutum. Ko da mutum ya ji shi a maƙogwaronsa ba zai karya masa azumi ba," a cewar malamin.

5) Maganin ciwon ido

Haka nan, amfani da maganin da ake ɗigawa a ido saboda wani ciwon ba shi karya azumi, in ji Sheikh Maihula.

"Ko da kuwa mutum ya ji shi a maƙogwaronsa ba zai karya azumi ba, saboda ba abinci ba ne, ba abin sha ba ne kuma ba shi kai wa ciki."