Premier League: West ham ta doke United, Chelsea ta yi nasara kan Newcastle

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta sha kashi a hannun West Ham United da ci 2-1 a wasansu da aka fafata a filin wasan London Stadium.

Wannan dai shi ne rashin nasara na huɗu da United ta yi a cikin wasanni tara da ta buga a kakar wasan bana, wanda ya ƙara maƙala alamar tambaya kan makomar kocinta Eric Ten Hag.

Yanzu dai ƙungiyar ta Old Trafford ta tsnici kanta a mataayi na 14 a teburin gasar bana.

A filin wasan Stamford Bridge kuma, Cole Palmer ya ci ƙwallonsa ta bakwai a kakar wasa ta bana a lokacin da Chelsea ta doke Newcastle da ci 2-1.

Nicolas Jackson ya fara jefa ƙwallo a ragar Newcastle a minti na 18 inda ya ci ƙwallonsa na biyar a wanna kakar wasan. Amma Alexander Isak ya farke a minti na 32.

A ƙarshe dai kwallon da Palmer ya ci wadda shi ne na bakwai cikin wasanni tara, ya bai wa Chelsea maki ukun da ya daukaka ta zuwa matsayi na huɗu a kan teburi.

Amma za ta iya komawa matsayi na biyar idan Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a karawar ta da Liverpool, amma kasancewar Chelsea a wannan matsayin na nuni ga irin ci gaban da ƙungiyar ta samu a ƙarƙashin koci Enzo Maresca ya zuwa yanzu.

Ta ci wasanni biyar cikin tara na gasar Premier ƙarƙashin tsohon kocin na Leicester, inda Manchester City da Liverpool ne kaɗai suka doke ta.

Ita kuwa Newcastle tana matsayi na 12 kuma ba ta yi nasara ba a wasanni biyar da ta yi a baya.