Fifa ta bayyana fili 12 da za a buga Club World Cup a Amurka a 2025

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar ƙwallon kafa ta duniya, Fifa ta sanar da fili 12 da za a gudanar da Club World Cup a Amurka a 2025.

Za a fara wasannin daga 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yulin 2025 a sabuwar gasar da aka sauya fasali da za a yi tsakanin ƙungiya 32.

Za a yi karawar a wasu daga manyan biranen Amurka, inda za a buga wasan karshe a MetLife Stadium a New Jersey, wato mil biyar tsakani da New York City.

Sauran filayen da za a gudanar da wasannin:

  • Mercedes-Benz Stadium, Atlanta
  • TQL Stadium, Cincinnati
  • Hard Rock Stadium, Miami
  • Geodis Park, Nashville
  • Bank of America Stadium, Charlotte
  • Camping World Stadium, Orlando
  • Inter&Co Stadium, Orlando
  • Rose Bowl Stadium, Los Angeles
  • Lincoln Financial Field, Philadelphia
  • Lumen Field, Seattle
  • Audi Field, Washington DC

Tuni Chelsea da Manchester City da Real Madrid suka samu shiga gasar kai tsaye, sakamakon lashe Champions League a tsakaninsu cikin shekara huɗu baya.

Haka Bayern Munich da Paris St-Germain da Inter Milan da Porto da kuma Benfica sun kai bante, sakamakon ƙwazon da suke yi a gasarsu da ta kai suna sawun gaba a kididdigar da ake kira co-efficient rankings.

Sauran ƙungiyoyin sun haɗa da shida daga Kudancin Amurka da 12 daga Asia da Afirka da kuma Arewacin Amurka da gurbi ɗaya da aka bai wa Oceania da na mai masaukin baƙi.

A baya ana buga Club World Cup a duk shekara da ta kan ƙunshi ƙungiya shida daga hukumar ƙwallon kafa bakwai daga nahiyoyin duniya.

Bayan da Fifa ta yanke shawarar faɗaɗa Club World Cup, an yi ta sukar tsarin daga ƙungiyoyi da ƴan wasa da masu ruwa da tsaki, saboda karin wasa biyu da ta yi a gasar.

Ƴan ƙwallo na korafin wasanni sun yi musu yawa, musamman da aka sauya fasalin Champions League da Europa League daga karawar rukuni da aka samu karin wasa biyu.

Ɗan wasan Manchester City, Rodri, wanda ya ji rauni da zai yi jinya har bayan kakar nan ya sanar a baya cewar ƴan wasa na daf da yin yajin aiki, sakamakon yawan wasannin da aka kara musu.