Ban tuntuɓi mahukuntan Man City ba kan barin Etihad - De Bruyne

Kevin de Bruyne

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne ya ce har yanzu bai tattauna da mahukuntan ƙungiyar ba kan barin Etihad a karshen kakar nan.

Ɗan kasar Belgium ya ce a shirye yake ya fuskanci sabon kalubale, ya kuma tattauna da iyalansa kan barin City, bayan da aka danganta shi da komawa Saudi Arabia a karshen kakar da ta wuce.

Mai shekara 33 ya koma Etihad a 2015 daga Wolsburg kaka ɗaya tsakani kafin a bai wa Pep Guardiola aikin horar da ƙungiyar.

A watan jiya Guardiola ya sanar cewar ba za su sayar da De Bruyne ba, kuma ɗan wasan tawagar Belgium ya ce bai tattauna da wasu ba kan sayar da shi ga wata ƙungiyar.

Saura kaka ɗaya ya rage wa De Bruyne a City, wanda ake hasashen za a kara tsawaita masa yarjejeniya a ƙungiyar da ke rike da Premier League na bara na huɗu a jere.

Manchester City ta haɗa maki tara, bayan da ta lashe dukkan wasa uku da fara babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana kamar yadda Liverpool ta yi wannan ƙwazon.

De Bruyne ya buga wa City dukkan karawa ukun da ta yi a bana, wanda ya ci ƙwallo ya kuma bayar da ɗaya aka zura a raga

Wanda Belgium ta gayyata buga Nations League da Israel da Faransa a watan nan, ya lashe Premier League shida da FA Cup biyu da League Cup biyar da Champions League.