Liverpool na duba yiwuwar ɗaukar Osimhen, Sevilla na son Depay

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Osimhen
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool na duba yiwuwar dauko dan wasan Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 25, idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa, sai dai makudan kudin da dan wasan da ke taka leda a Nepoli ke bukata ya yi musu tsada. (Corriere dello Sport - in Italian)

Dan wasan tsakiya na Newcastle Kieran Trippier ka iya komawa daya daga cikin kungiyoyin kasar Saudiyya, a daidai lokacin da dan wasan da ke tsarewa Ingila gida mai shekara 33 ya zaku ya bar kungiyarsa. (Sun)

Sai dai kungiyar Newcastle ta yi watsi da rade-radin cewa Trippier na son barin kungiyar domin komawa Saudiyya ko kasar Turkiyya. (Talksport)

Tsohon dan wasan Chelsea da Fulham, Willian, mai shekara 36, ya garzaya birnin Athens inda Olympiakos ke fatan daukar dan wasan na asalin Brazil. (Fabrizio Romano)

Da alama Sevilla na tuntuba da taya dauko dan wasan gaba na Memphis Depay, mai shekara 30, wanda ke daukar hankalin kulub din turai tun bayan ficewarsa daga kungiyar Atletico Madrid. (Marca - in Spanish)

Dan wasan gaba na Ingila Ivan Toney, mai shekara 28, zai dinga daukar fam dubu 403,000 a kowanne wata, adadin abin da ya ke dauka kafin harajin da Ingila ke laftawa shi ne fam 800,000 a kowanne mako bayan komawa kungiyar Al-Ahli, daga Brentford. (Mirror)

Mai tsaron gida na Northern Ireland, da ke taka leda a Newcastle Jamal Lewis, 26, na gab da komawa kulub din Brazil na Sao Paulo (Belfast Telegraph)

Roma ma na gab da kammala yarjejeniyar dauko mai tsaron gida na Sifaniya Mario Hermoso, 29, wanda zai bar kungiyar Atletico Madrid a kakar nan. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)

Har yanzu dan wasan gaba na Oxford Mark Harris, 25, a kasuwar sabbin 'yan wasan Bundesliga irinsu Holstein Kiel, wanda ya ke kokarin ganin samun kungiya kafar karshen kakar nan. (Sun)

Roma na ci gaba da tattauna kan tsohon dan wasan Jamus kuma na tsakiyar Borussia Dortmund, Mats Hummels, 35,sakamakon neman wanda zai maye gurbin mai tsaron gida na Ingila Chris Smalling, 34, wanda zai koma Pro League ta Saudiyya, wato Al-Fayha. (Sky Sports Italia)