Manyan ƙungiyoyin Premier na rububin Nico Williams, Barca na nazarin Isak

Nico Williams

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto, Nico Williams ya taimaka wa Spain lashe gasar Kofin Euro 2024
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid na son ɗaukar ɗan wasan Liverpool da Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, a matsayin kyauta. (Telegraph)

Arsenal da Chelsea da Liverpool da kuma Tottenham na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan gefe na ƙasar Sifaniya Nico Williams mai shekaru 22.

Liverpool na shirin miƙa tayin Fam miliyan 91 kan ƴan wasa biyu a wata Junairu. Ɗan wasan baya na Bournemouth Milos Kerkez mai shekara 21 da kuma ɗan wasan tsakiya na Real Sociedad Martin Zubimendi mai shekara 25, (Teamtalk)

Barcelona na nazari kan ɗan wasan gaba na Newcastle United da Sweden Alexander Isak, Mai shekara 25. (Caught Offside)

Manchester United ta bayyana sha'awar sayen ɗan wasa baya na RB Leipzig da Jamus David Raum mai shekara 26 da kuma ɗan wasan gaban Juventus da Turkiyya Kenan Yildiz mai shekara 19. (Sky Germany)

Manchester United ta tuntuɓi ɗan wasan baya na ƙasar Kanada Alphonso Davies domin ganin yiwuwar komawarsa kulob ɗin bayan kwatiraginsa da Bayern Munich ya ƙare a bazara mai zuwa.

Barcelona za ta yi gogayya da Real Madrid kan ɗan wasan bayan Manchester United da Portugal Diogo Dalot, idan ɗan wasan mai shekara 25 ya nuna alamun barin Old Trafford. (Caught Offside)

Tsohon Kocin Manchester United Erik ten Hag ya kasance cikin jerin sunayen masu horaswa da RB Leipzig ke nazari a kai. (Sky Germany)

Ɗan wasan Ivory Coast Amad Diallo mai shekara 22 na iya barin Manchester United a watan Junairu sakamakon rashin cimma yarjejeniya da kulob ɗin na Old Trafford. (Express)

Tottenham da Manchester City da Chelsea suna rububin ɗan wasan tsakiya na AC Milan da Netherlands, Tijjani Reijnders mai shekara 26. (Calciomercato)

Tsohon kocin Juventus da AC Milan Massimiliano Allegri na cikin waɗanda ke Iya zama Kocin West Ham idan Hammers ta kori Julen Lopetegui. (Calciomercato)