Isra'ila ta wuce wa'adin da Amurka ta ƙayyade na bunƙasa agaji a Gaza - MDD

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Jon Donnison
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Jerusalem
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Babbar hukumar bayar da agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Gaza ta ce Isra’ila ta gaza ƙetara wa’adin da Amurka ta gindaya na ko ta bunƙasa agajin da ake kai wa yankin ko kuma ta fuskanci ragi a tallafin sojin da ta ke samu daga Amurka.
A watan da ya gabata, a wata wasika mai kakkausar lafazi, sakataren harkokin wajen Amurka, ya bai wa Isra'ila wa'adin kwanaki 30 don tabbatar da ƙarin motocin dakon kayan agaji na isa Gaza a kullum. Ranar Talatar da ta gabata ne wa’adin ya cika
Adadin tallafin da ake samu a Gaza ya kasance mafi ƙanƙanta a cikin shekara guda, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya. Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar fuskantar matsananciyar yunwa a arewacin Gaza, inda ba a kai wani agajin a-zo-a-gani ba a cikin watan da ya gabata.
Isra'ila ta ce ta ƙara yawan taimakon da ake kai wa Gaza, kuma ta zargi hukumomin agajin da ke Gaza rarraba agajin yadda ya kamata.

A cikin wasiƙar da ya rubuta a ranar 13 ga watan Oktoba, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce ya kamata Isra’ila ta riƙa barin aƙalla manyan motocin dakon kaya 350 a kowace rana zuwa cikin Gaza, a kullum, nan da 12 ga watan Nuwamba.
Amma da aka tambaye shi ko Isra'ila ta yi abin da ya dace tun lokacin don cimma wannan burin na Amurka, Louise Wateridge, Babbar Jami'ar gudanar da agajin gaggawa a Gaza na hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ƴan gudun hijirar Falasdinu (UNRWA), ba tare da wani tantama ba ta ce "A'a".
“Babu isassun agaji a nan. Babu isassun kayayyaki,” kamar yadda ta shaida wa BBC daga sansanin UNRWA da ke tsakiyar Gaza.
“Mutane na fama da yunwa a wasu yankunan. Mutane suna jin yunwa sosai. Suna kokawa kan buhunan garin filawa. Babu isassun kayayyakin abinci.”
A cikin wani bidiyo da wani ɗan jarida a Gaza ya yi wa BBC, a ɗaya daga cikin ƴan gidajen burodin da suka rage a tsakiyar zirin, ana iya ganin burodi mai zafi da ke fitowa daga cikin tanda a kan bel ɗin jigilar kaya.
Ta cikin wata ƙaramar taga, hannaye suka kama jakunkunan burodi yayin da suke miƙa kudi.
Kamar kowane abinci, farashin burodi ya yi tashin gwauron zabi a cikin shekarar da ta gabata.
A wajen gidan burodin, ɗaruruwan mutane ne suka yi ta tururuwa inda suke kokawa domin samun damar karɓar burodin.
Daga cikinsu akwai wata kaka, Aida al-Horan, wadda kuma ta ke karɓar miya.
"Idan ba don wurin bayar da agajin abincin nan ba, da mun mutu da yunwa," in ji Aida.
“Kowace rana gwagwarmaya iri ɗaya ce. Ina kai wa da komowa zuwa wurin karɓar abincin."

Asalin hoton, EPA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma a cikin wata ɗaya da ya gabata, Isra'ila ta cika buƙatar Amurka na buɗe ƙarin wata mashiga zuwa Gaza.
Cogat - Ƙungiyar sojojin Isra'ila da ke da alhakin ayyukan jinƙai a zirin Gaza - ta sanar a safiyar Talata cewa ta buɗe wata sabuwar mashigar Kissufim zuwa kudancin yankin.
Wani mai magana da yawun Cogat ya shaida wa BBC cewa "akasarin abubuwan [buƙatun Blinken] an cimma su kuma waɗanda ba samu an yi ba ana kan tattaunawa a kansu, [kuma) wasu buƙatun na Amurka sun shafi batutuwa ne da aka riga aka warware."
A Zikim, da ke gefen iyakar Isra'ila na ɓangaren arewa, na kusanci Gaza kamar yadda ban taɓa yi ba cikin fiye da shekaru 10.
Na kasance wakilin BBC a Gaza tsakanin shekarun 2009 zuwa 2013 kuma na san zirin da kyau.
Amma tun da aka fara wannan yaƙin, Isra'ila ba ta bai wa ƴan jarida damar shiga Gaza ba tare da wani matsatsi ba.
Zikim na ɗaya daga cikin mashigan da Isra'ila ta sake buɗewa a ƴan makonnin nan.
A wata hirar bidiyo da sojojin Isra'ila suka shirya a ranar Litinin, kwana guda gabanin cikar wa'adin Amurka, an gayyace ni da wasu ƴan jarida mu ɗauki bidiyo a kusa da motocin agaji guda takwas da ke wucewa cikin Gaza.
An jibge su shaƙe da buhunan filawa da shinkafa da tolifefa da dai sauransu.
Don haka, agaji yana shiga Gaza.
Amma dai abin da ake samu bai kai yadda ake buƙata ba.

Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ayyukan jinƙai (OCHA) ya ce, a cikin watannin da suka gabata, matsakaicin adadin manyan motocin da ke shiga cikin zirin ya wuce motoci 40 a kowace rana.
Isra'ila ta yi jayayya da alƙaluman na OCHA tare da ɗora wa Majalisar Dinkin Duniya laifin gaza kai kayan agajin.
Ta ce daruruwan buhuhunan kayan agaji na jira a karɓo su daga hukumomin agaji a gefen iyakar Gaza kuma ta ce wasu mutane ɗauke da makamai suna sace wasu motocin agajin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ki amincewa da hakan.
Ta ce alhakin Isra'ila ne a matsayinta ta mai madafan iko da ta sauƙaƙe shigar da kayan agaji cikin aminci a cikin Gaza.
Ta jaddada cewa ba za ta iya rarraba kayan agaji ba saboda haɗarin da ke tattare ayyukan sojin da Isra'ila ke gudarwa.
Sama da shekara guda Isra'ila ta shafe ta na aikata abubuwan da suke wuce gona da iri a idon Amurka
Yawancin barnar da Isra'ila ta yi makaman Amurka ne suka haifar, wanda ta bai wa Isra'ila don taimaka mata a yaƙin da ta ke yi da Hamas bayan harin 7 ga watan Oktoba 2023.
Amma a cikin kwanakin ƙarshe na shugabancin Biden kuma yayinda aka yi asarar rayukan Falasdinawa sama da 43,000, da wuya Fadar White House za ta iya ɗaukar tsauraran matakan daƙile tallafin kayan yaƙin da ta ke bai wa Isra'ila.














