Tsofaffin abokan hamayyar Trump sun mara masa baya

Tsofaffin abokan neman takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican sun hada kai tare da nuna goyon bayansu ga Donald Trump, wanda ya samu takarar, a dare na biyu na babban taron jamiyyar.
Abokan hamayyar sun rika yabawa da koda Trump a kan manufofinsa na tattalin arziki da bin doka da oda da kuma musamman kan baki ko shige da fice.
Tsofaffin abokan hamayyar na neman yi wa jamiyyar Republican din takarar shugaban kasa, a zaben watan Nuwamba wadanda Donald Trump ya kayar da su, sun zubar da makamansu, inda daya bayan daya suka rika fita fage, a daren da ya kasance na biyu daga cikin kwana hudu da za a shafe ana wannan babban taro, suna koda tsohon abokin hamayyar tasu, wanda a yanzu ya samu zama gwanin da zai yi wa jam'iyyar takara.
Daga wajen da yake zaune, da ke sama da dandamalin taron Trump, wanda ya tsallake rijiya da baya daga yunkurin hallaka shi da wani dan bindiga ya yi ranar Asabar, ya rika murmushi jifa-jifa yayin da yake kallon tsofaffin abokan hamayyar tasa, Nikki Haley, tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, wadda sai da tafiya ta yi tafiya ta zubar da makamanta daga takarar, da Ron Desantis da kuma dan kasuwa Vivek Ramaswamy, suna tabbatar masa da cikakken goyon baya ga takarar tasa.
Nikki Haley, matar da a baya a lokacin fafutukar neman takarar ta ce karin shekara hudu na Trump zai haddasa hatsaniya sai ga ta kuma a Talatar nan tana bayyana sabanin kalaman.
Ta danganta da abin da ta kira barazana ga ‘yancin Amurka, daga shugabancin Democrat, tana cewa manufofin Trump za su tabbatar da zaman Amurka lafiya cikin tsaro, kamar yadda ta ce ya yi a baya.
Ta ce Trump ne da kansa ya bukaci ta yi jawabi a gangamin na Milwaukee da zummar hadin kai.
Shi ma dan kasuwa Vivek Ramaswamyamy, wanda bai ja da takarar kamar Haley ba, ya tabbatar da goyon bayansa ga Trump din.











