Bayanai kan Thomas Matthew Crooks mutumin da ake zargi da harbin Trump

…

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI ta bayyana sunan mutumin da ya harbi Donald Trump a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Hukumar ta FBI ta ce mutumin sunansa Thomas Matthew Crooks.

Ana zargin Crooks da buɗe wuta a lokacin da tsohon shugaban na Amurka ke yi wa jama'a jawabi a garin Butler na jihar Pennsylvania, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu mutane biyu.

Jami'ai sun bayyana cewar ƙwararrun masu harbi da bindiga na Hukumar Leken Asiri sun harbe mutumin mai shekara 20.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta FBI ta fitar ta ce Crooks ne “mai hannu” a yunƙurin kashe tsohon shugaban ƙasar kuma ana gudanar da bincike.

Kasancewar ba ya ɗauke da wata shaida da ke nuna bayanansa, masu bincike sun yi amfani da ƙwayoyin halitta wajen gano shi kamar yadda hukumar ta FBI ta bayyana.

Ya fito daga Bethel Park a Pennsylvania kimanin kilomita 70 (mil 43) daga Butler, (wurin da aka yi yunkurin kisan), kuma da alama ya kammala karatunsa a shekarar 2022 daga makarantar Bethel Park a cewar jaridar Pittsburgh Tribune-Review.

Bayanan masu kaɗa ƙuri'a na jihar sun nuna cewa Crooks ɗan jam'iyyar Republican ne kamar yadda kafofin yada labaran Amurka suka bayyana.

An kuma bayar da rahoton cewa ya ba da gudummawar dala 15 ga gidauniyar yaƙin neman zaɓe masu sassaucin ra'ayi ta ActBlue a shekara ta 2021.

Mene ne dalilinsa?

Hukumomi na bincike kan abin da ya sa ya kai harin, tare da duba yiwuwar hannun wani

"A halin yanzu ba mu da wani takamaiman dalili," in ji Kevin Rojek wakili na musamman a hukumar FBI da ke Pittsburgh, yayin wani taron tattaunawa a daren Asabar.

Binciken abin da ya faru zai iya ɗaukar watanni kuma masu binciken za su yi aiki ba tare da gajiyawa ba har sai sun gano manufar Crooks in ji Mista Rojek.

Da yake magana da CNN mahaifin Crooks Matthew Crooks ya ce yana ƙoƙarin gano abin da ya faru amma zai jira har sai ya yi magana da jami'an tsaro kafin ya ce wani abu kan ɗansa.

Akwai wanda ya mutu?

…

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bidiyon kafar yada labaran TMZ a Amurka ya nuna wani ɗan bindiga a saman gini yana buɗe wuta

Kafar labarai ta CBS ta ce an kashe mutum guda tare da jikkata wasu biyu a lamarin. Dukkanin mutanen uku da abin ya shafa maza ne ƴan kallo, amma ba a bayyana sunayensu ba.

A wani sakon da ya wallafa a dandalinsa na 'True Social', Mista Trump ya ce an harbe shi da harsashi wanda ya huda saman kunnensa na dama.

"Na san cewa wani abu ya faru saboda na ji sautin harbe-harbe, kuma nan da nan na ji harsashin ya ratsa min fata, kuma jini da yawa ya fita don haka sai na gane abin da ke faruwa."

Jini ya bayyana a kunne da fuskar Trump yayin da jami’an tsaro suka fitar da shi daga cikin taron.

Trump yana "samun sauƙi kuma yana godiya", a cewar wata sanarwa da aka buga a shafin sada zumuntar kwamitin jam'iyyar Republican (RNC).

Ya tazarar ɗan bindigar take daga inda Trump yake?

…

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya ga wani mutum da ake kyautata zaton Crooks ne ɗauke da bindiga a rufin gini kafin a harbi Trump.

Sashen tantance labarai na 'BBC Verify' ya nazarci faifan bidiyon tare da tabbatar da cewa ɗan bindigar ya buɗe wuta ne daga saman wani gidan ajiyar kaya da bai wuce mita 200 daga inda tsohon shugaban ƙasar yake ba.

Hotunan bidiyo da TMZ ta samu ya nuna lokacin da aka fara harbin.

Maharin ya buɗe wuta da "bindiga samfurin AR", kamar yadda kafar yaɗa labaran CBS, abokiyar huldar BBC a Amurka ta ruwaito.

Sai dai hukumar FBI ta ce ba za ta iya tantance irin makaman da ɗan bindigar ya yi amfani da su ba ko kuma sau nawa ya harba.

Hukumar ta ce wani ƙwararren maharbi a hukumar leken sirri ne ya mayar da martani tare da kashe ɗan bindigar.

Daga baya hotuna sun nuna yadda wasu jami'ai ɗauke da makamai suka nufi wata gawa a kan rufin ginin.