Abin da ya faru a wasannin Premier League a ƙarshen mako

An wallafa

A karshen makon nan babu wasannin lig a wasu kasashen, saboda za a fafata tsakanin kasa da kasa a jadawalin kalandar Fifa.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware wasu ranaku a kakar tamaula da za a buga ko dai wasan sada zumunta ko karawar neman shiga gasar kofin nahiyoyi ko na duniya.

A karshen mako aka kammala fafatawar mako na takwas a gasar Firimiya ta Ingila - ga jerin abubuwan da suka faru a wasannin.

Tottenham

Tana matakin farko a kan teburin Firimiya da maki 20, bayan da ta je ta ci Luton Town 1-0 ranar Asabar.

Duk da Tottenham ta rasa Harry Kane kafin fara kakar bana, wanda ya koma Bayern Munich, amma rashin sa bai nuna ba a kungiyar.

Tuni sabon koci, Ange Postecoglou ya sauya salon wasan kungiyar, wadda ke cin ƙwallo biyu ko fiye da hakan, wadda har yanzu ba ta yi rashin nasara ba a karawa takwas a Premier League.

Wasa da Luton ne kawai Tottenham ta ci 1-0 a bana.

Arsenal

Karon farko Gunners ta yi nasara a kan Manchester City a shekara takwas, bayan da ta ci 1-0 a ranar Lahadi.

Wannan kwazon da Arsenal ta yi ya tabbatar da cewa tana cikin wadanda ake sa ran za su iya lashe kofin Firimiya a bana sun ƙuma kara samun kwarin gwiwa.

Gunners tana ta biyu da maki iri ɗaya da Tottenham, ita ma har yanzu ba a doke ta ba a bana a Firimiya kawo yanzu.

Liverpool

Liverpool ta ci karo da koma baya, wadda ta tashi 2-2 a gidan Brentford, kafin nan Tottenham ta yi nasara a kan Liverpool 2-1 a Premier League.

Kungiyar Anfiield na bukatar kara sa kwazo, wadda wasu wasan ita ke fara ci daga baya a farke - ya kamata ta kara karfi a gurbin masu tsare mata baya.

Aston Villa

Villa ta yi rashin nasara a hannun Newcastle da Liverpool amma ta caskara Brighton 6-1 -- hakan na nufin kungiyar za ta iya taka rawa a kakar nan idan ta yi kokari ta dinke ɓarakarta.

To sai dai kungiyar ta je ta tashi 1-1 da Wolverhampton a Molinuex.

Manchester City

City ce ke rike da kofin Firimiyar Ingila na bara, wadda ke fatan daukar na hudu a jere, amma ta ci karo da koma baya a wasa biyu da suka gabata baya.

Arsenal ta doke City 1-0 ranar Lahadi a Emirates, kafin nan Wolverhampton ce ta fara yin nasara a kan kungiyar Etihad da ci 2-1.

Ita dai Wolves karawa daya ta yi nasara daga biyar a baya a lokacin da ta karbi bakuncin City, amma ta sa kwazo ta hada maki uku a karawar.

City na fatan Rodri zai koma buga mata wasan gaba, bayan dakatarwar jan kati da aka yi masa a wasan Tottenham.

Brighton

Ba ta kokari a gasar zakarun Turai sosai, wadda ta yi nasara a hannun West Ham da Aston Villa a gasar Firimiya.

Ranar Lahadi Brighton, wadda Villa ta sharara mata kwallo 6-1 ta tashi 2-2 da Liverpool.

West Ham

Bayan nasara a wasa hudu daga karawa takwas a Premier League a kakar nan, ba a kallon rashin nasarar da kungiyar ta yi a bana a hannun Manchester City da Liverpool.

David Moyes wanda ya fuskanci kalubale a kakar da ta wuce, ya tashi 2-2 a gida da Newcastle United ya raba maki da ita ke nan.

Crystal Palace

Jadawalin bana ya zo wa kungiyar da sauki a bana a wasannin farko-farko, amma ba ta amfana ba a fafatawar da ta yi da Forest da Fulham da kuma Brentford.

Bayan da da Manchester United ta fitar da ita a gasar cin kofin Carabao, sai kuma ta ci United 1-0 a Firimiya, sai kuma ta tashi 0-0 da Forest.

Wolves

Bayan da ta sauya koci daf da za a fara kakar bana, ana ganin sauyi a kungiyar wadda ta yi nasara a kan Everton da doke Manchester City a gida.

Ke nan kungiyar ta ƙara samun kwarin gwiwar cewar za ta iya fuskantar kowacce kungiya ba tare da fargaba ba.

Fulham

Wannan kungiyar za ta ci gaba da zama cikin 'yan tsaka-tsakin teburi, wadda kungiyoyin da ke kasan teburi take iya lallasawa, amma da zarar ta shiga hannu manya sai buzunta.

Forest

Steve Cooper na son kara kwazo kan yadda yake jan ragamar kungiyar, wadda take da maki tara, kwazon da ya zarta wanda ta yi a bara a irin wannan lokacin.

Everton

Magoya baya sun fara sa ran cewar kungiyar za ta fada Championship a karshen kakar bana, wadda ba ta iya cin wasa ba har da wanda take bugawa a gida.

To sai dai wasu 'yan wasan na warkewa daga jinya, watakila kungiyar ta tabuka nan gaba, amma idan ba a samu sauyi ba za ta iya barin gasar Firimiya a karshen kakar nan.

Luton

Ba wanda ya bai wa kungiyar damar cewar za ta iya taka rawar gani a bana, wadda take da maki hudu daga karawa takwas.

Wadda ta doke Everton a Goodison Park - hakan na nuna cewar akwai fata mai kyau nan gaba kadan.

Manchester United

Ba don an saka Scott McTominay a wasan ba ranar Asabar da Brentford ta yi nasara a kan United, waddda ka iya fadawa cikin matsi.

An doke United a wasa hudu, ta yi nasara a hudu, tana tsakiyar teburi, idan har tana son ta sake komawa Champions League a baɗi sai ta ƙara kwazo.

Raunin da 'yan wasan United da yawa ke fama da shi ya kai wa kungiyar koma baya, amma bayan da ta kare a bara da Carabao Cup da yin ta uku a teburin Firimiya, fatan da ake mata a bana yana da yawa.

Newcastle

Ana sa ran kungiyar tana cikin wadanda za ayi rububin lashe kofin Firimiya da ita, musammam da ta doke Sheffield United 8-0.

Sai dai kungiyar ta ci karo da koma baya, bayan da Brighton ta doke ta, da kuma tashi 2-2 a gidan West Ham United.

Amma kungiyar tana kan turbar lallai za ta iya yin abin kirki a kakar nan.

Chelsea

Kungiyar da Mauricio Pochettino ke jan ragama ta fara komawa kan ganiya bayan da ta yi nasara a wasa biyu a jere.

Chelsea ta doke Fulham da Burnley. To amma akwai jan aiki a gabanta, wadda za ta fuskanci Arsenal da Tottenham da Manchester City da Newcastle da kuma Manchester United a wasa shida nan gaba.

Daga nan za a tantance ko Chelsea ta koma kan ganiya.

Brentford

Rashin Ivan Toney ya fara nuna kungiyar, wadda ta yi wasa shida ba tare da yin nasara ba kawo yanzu.

Ta zura kwallo 11 a raga, an zuba mata 12, wadda take ta 15 a teburi da cin wasa daya, aka doke ta karo uku, sannan ta yi canjaras hudu.

Hakan na nufin akwai jan aiki a gabanta.

Wadanda suke kasan teburin Premier League

Burnley

Bayan da ta lashe Championship ta samu gurbin shiga Premier League a bara, sai ga kungiyar ta kasa taka rawar gani a wasannin bana.

An yi wa Vincent Kompany hangen cewar zai yi kokari sosai a gasar, wanda yake da kwarewa a lokacin da ya taka leda a Manchester City.

Kawo yanzu an ga raunin kungiyar wadda aka zura wa kwallo 20 a wasa takwas bayan fara kakar nan.

Bournemouth

Matakin da kungiyar ta dauka na maye gurbin Garry O'Neil da Andoni Iraola, bai kawo ci gaba ba, illa gagarumar koma baya.

O'Neil ne ya ceci kungiyar a bara ta tsallake komawa buga karamar gasa.

Har yanzu kungiyar ba ta ci wasa ba, sannan 'yan kwallon sun kasa komawa salon da sabon kocin ke bukatar gani.

Kungiyar tana da matsalar mai cin kwallo tana daga cikin wadanda ba su zura da yawa a raga ba.

Sheff United

Maki daya daga karawa takwas da fara kakar bana a Firimiya ba sakamako ba ne mai kyau.

Sannan za ta fuskanci Manchester United da Arsenal a jere da zarar an kammala wasannin kasa da kasa, ke nan za ta ci gaba da rashin nasara.

Tuni aka fara rade-radi kan makomar koci, Paul Heckingbottom, bayan da kungiyar ke matakin karshe da ake gani kamar ta samu gurbin zama ke nan.