Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saka ba zai buga wa Ingila wasa da Austalia da Italiya ba
Dan kwallon Arsenal, Bukayo Saka ba zai yiwa tawagar Ingila wasa biyu da za ta kara nan gaba ba, in ji koci Mikel Arteta.
Saka, wanda ke jinya bai buga wa Arsenal gasar Premier League ba ranar Lahadi da ta doke Manchester City a Emirates.
Ingila za ta kece raini da Austalia ranar 13 ga watan Oktoba, sannan kwana hudu tsakani ta fafata da Italiya a wasan neman gurbin shiga gasar nahiyar Turai.
Rashin buga wasa da Saka bai yi ba ranar Asbar an kawo karshen karawa 87 a jere da ya yi a Premier League da Arteta ke saka dan kwallon mai shekara 22.
Matashin na fama da raunin da ya sa aka sauya shi a wasan Champions League da suka buga da Lens inda suka yi nasara da ci 2-1 ranar Talata, aka kuma cire shi a wasa da Bournmouth.
A ranar ta Lahadi Arteta ya yi nasara a kan Manchester City a karon farko a wasa takwas da ya fuskanci kungiyar.
Haka kuma Arsenal wadda ba a doke ta ba a bana a Premier League ta kawo karshen wasa 12 a jere da City ke yin nasara a kanta a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Arsenal mai maki 20 iri daya da na Tottenham tana ta biyu a teburin Premier League, yayin da Tottenham ce ke jan ragama.