Monaco na daf da daukar Balogun daga Arsenal

Balogun

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan wasan gaba na Arsenal Folarin Balogun na daf da komawa Monaco kan kudi fam miliyan 35 duk da sha'awar da Chelsea da Inter Milan suka bayyana kan dan wasan.

Ana ci gaba da tattaunawa amma ana sa ran dan wasan mai shekaru 22 zai koma Faransa, inda ya taka rawar gani a zaman aro da ya yi a Reims a bara.

A halin da ake ciki kuma ana sa ran dan wasan bayan Arsenal Kieran Tierney zai koma Real Sociedad a matsayin aro na tsawon kakar wasa guda.

Dan wasan dan kasar Scotland mai shekara 26 ya buga wa Gunners wasa fiye da sau 120 tun lokacin da ya koma Celtic a shekarar 2019, amma ya buga gasar Premier sau shida kacal a bara.

Balogun ya taka rawar gani a gasar Ligue 1 ta Faransa a bara, inda ya ci wa Reims kwallo 22.

Arsenal ta yi farin cikin sauraron tayin da ake yi wa dan wasan wanda ba a tunanin yana cikin tsarin Mikel Arteta.

Ya zuwa yanzu dai ba a saka shi cikin ‘yan wasan Premier ba duk da cewa Gabriel Jesus ya ji rauni.

Eddie Nketiah ne ya fara wasanni biyu na farko na kakar wasan bana, inda Arsenal ta doke Nottingham Forest a karshen mako kafin ta samu nasara kan Crystal Palace don lashe wasanninta biyu na farko.