Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan tawayen Colombia sun sako mahaifin Luis Díaz
Majiyoyin ‘yan sanda da kafafen yaɗa labarai na ƙasar Colombia sun bayyana cewa ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da mahaifin ɗan ƙwallon Liverpool Luis Díaz na tsawon kwanaki 13 sun sako shi.
Jami’an rundunar 'yan tawaye na ELN sun miƙa Luis Manuel Díaz ga Jami’an Majalisar Dinkin Duniya da jami’an cocin Katolika.
An sace shi ne a ranar 28 ga Oktoba a garinsu, Barrancas.
An kuma kama mahaifiyar ɗan wasan, amma an sako ta cikin 'yan sa'o'i.
Kafofin yaɗa labaran cikin gida sun ce Mista Díaz na tafiya ne da helikwaftan soji zuwa birnin Valledupar, inda za a duba lafiyarsa kafin a mayar da shi ga iyalansa.
Har ila yau, sun ambato hukumomi na cewa yana cikin ƙoshin lafiya, ba tare da wata alamar cewa an muzanta shi ba.
A cewar jaridar El Tiempo, an yi ta murna a unguwar da su Mista Diaz ke zaune, inda 'yan uwa suka hau motocinsu domin su ratsa kan tituna suna murna.
Yawancinsu suna sanye da rigar ƙungiyar Liverpool mai lamba 23 da sunan Luis Díaz.
Satar da aka yi ya haifar da zulumi a Colombia, inda Luis Díaz - wanda ke cikin tawagar ƙasar Colombia - ya shahara matuka.