Ku San Malamanku tare da Malam Idris Yunus Limamin masallacin Gwarimpa

Ku San Malamanku tare da Malam Idris Yunus Limamin masallacin Gwarimpa
An wallafa

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya, kuma limamin masallacin Juma'a na Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa da ake kira Abdullateef Adegbite da ke birnin tarayyar Abuja.

Malamin, ya ce shi cikakken haifaffen Kano kuma ya yi karatu a makarantu daban-daban a jihar.

Ya ce ya yi karatun allo a wata makarantar Malan Sani da ke unguwar Birdget, daga nan ya koma karatu wajen marigayi Malam Mahmoud Ilyasu Dokoki, kuma shi ne wanda ya fi tasiruwantuwa d karatunsa.