Matashin da ya daina zuwa makaranta ya zama na uku mafi arziki a duniya

Gautam Adani is is the world's third richest man - behind Elon Musk and Jeff Bezos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gautam Adani shi ne mutum na uku mafi karfin tattalin arziki a duniya - bayan Elon Musk da Jeff Bezos
An wallafa

A daren ranar 26 ga watan Nuwamban 2008, Gautam Adani, mutum na 10 mafi arziki a Indiya, na cin abincin dare a wata maciya da ke birnin Mumbai a otel ɗin alfarma na Taj Mahal, lokacin da ya hangi 'yan bindiga na kutsa kai tare da buɗe wuta ta ko ina da kuma cilla gurneti.

'Yan bindigar 10, dukkansu 'yan Pakistan, sun je wurin ne ta ruwa, suka rarrabu rukuni-rukuni, suka ƙwace ababen hawa kuma suka kai harin, ciki har da otel biyu na alfarma.

Harin da aka shafe tsawon awa 60 ya jawo kisan mutum 166 kuma ya lalata alaƙa tsakanin Pakistan da Indiya.

Daga baya Mista Adani ya faɗa wa Mujallar India Today cewa wani ma'aikacin otel ɗin ne ya tattara mutane a gidan ƙasa tsawon awanni sannan ya mayar da su cikin wani ɗaki a kan bene a daidai lokacin da ake tsaka da tirka-tirkar a waje.

Bayan shafe tsawon dare a cikin ramin, an kwashe Mista Adani da sauran mutanen ta wata ƙofar baya bayan dakaru sun kewaye otel ɗin baki ɗayansa da safe.

"Na hangi mutuwa daga nisan ƙafa 15," kamar yadda ya faɗa wa 'yan jarida bayan ya koma Ahmedabad a jirginsa a ranar.

Shekara 14 bayan haka, Mista Adani mai shekara 60 a yanzu, shi ne na uku mafi arziki a duniya - bayan Elon Musk da Jeff Bezos.

Ya mallaki gamayyar kamfanonin makamashi bakwai, da ma'aikata 23,000 da kuma jarin da ya zarta dala biliyan 230.

An yi ta ambatar sunansa a rahotanni a makon nan saboda yana gab da sayen gidan talabijin na NDTV, kafar labaran Indiya da aka fi girmamawa, a yunƙurinsa na shiga harkokin yaɗa labarai na farko.

Tun kafin ɗan gudun makarantar ya zama biloniya, Mista Adani ya taɓa tsallake rijiya da baya. A watan Janairun 1998, an ruwaito cewa an yi garkuwa da shi da wani abokin harkarsa don karɓar kuɗin fansa a motarsu da wani rukunin 'yan bindiga suka yi a Ahmedabad.

An saki biyu daga cikin waɗnda ake zargi a 2018 saboda ɗan kasuwar da abokinsa "ba su taɓa zuwa kotun ba don ba da shaida duk da sammacin da kotun ta dinga yi musu".

Bayan ya daina zuwa makaranta lokacin da yake shekara 16, Mista Adani ya koma Mumbai don ya fara sana'ar cinikin gwal. Sai dai bai daɗe ba, inda ya koma jiharsa Gujrat bayan shekara biyu don yin aiki a ma'aikatar ƙunshe kayayyaki da ɗan uwansa ke jagoranta.

Mista Adani ne ya mallaki tashar lantarki mai amfani da gawayin kwal a Gujrat

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto, Mista Adani ne ya mallaki tashar lantarki mai amfani da gawayin kwal a Gujrat
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Iyayen Adani masu rufin asiri ne da ke harkar tufafi, kuma ya kafa kamfaninsa na farko a 1998 da ke kasuwancin kayayyaki. Shekara 24 bayan haka, kamfanoninsa da ke fama da bashi sun haɓaka zuwa tashoshin jirgin ruwa, da hakar ma'adanai, da layukan dogo, da ayyukan raya ƙasa, da kuma harkokin gine-gine, abin da ya sa wani mai sharhi ya siffanta shi da "ba mamaki mafi hazaƙa cikin masu kuɗin Indiya na zamanin nan".

Shi ne ke da kamfanin siminti na biyu mafi girma a Indiya - da tashoshin gaɓar ruwa 13 cii har da mafi girma a ƙasar da ke yammacin garin Mundra - kuma yana aiki da filayen jirgi bakwai. Yanzu haka yana gina titi mafi tsayi a Indiya daga Delhi zuwa Mumbai, birnin kasuwancin ƙasar.

Saboda mallakar tashoshin samar da lantarki shida da ya yi, Adani ne ɗan kasuwa mafi girma a harkar lantarkin Indiya. A lokaci guda kuma, ya yi alkawarin zai zuba jarin dala biliyan 50 a makamashi maras gurɓata muhalli sannan yana gudanar bututun iskar gas mai tsawon kilomita 8,000. Ya sayi wuraren hakar kwal a Indonesiya da Australiya. Yana so ya zama ɗan kasuwar makamashi mai tsafta mafi girma nan da 2030.

"Saboda ya kasa samun abin da yake so na more rayuwa a Indiya, sai ya gina layukan jirgin ƙasa da kansa da tashoshin lantarki. Da ya ga babu mahaƙar kwal a Indiya sosai, sai ya saye su a Indonesiya da Australiya kuma yake shigar da kayayyakinsu Indiya," a cewar marubuci Mista Mr Crabtree.

An yi zanga-zanga a Australiya a 2019 kan mahaƙar kwal ta Mista Adani da ke tsakiyar Queensland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi zanga-zanga a Australiya a 2019 kan mahaƙar kwal ta Mista Adani da ke tsakiyar Queensland

Mista Adani ya jawo ce-ce-ku-ce a tsawon wannan lokaci. Alƙarsa da Firaminista Narendra Modi tun lokacin da yake babban ministan Gujrat, da kuma yanzu da yake firaministan Indiya. Hakan ta sa wasu ke kwatanta harkokin kasuwancinsa a matsayin na jari hujja kawai.

"Mutanen biyu sun ji daɗin harkokinsu. Dokokin kasuwanci da Mista Modi ya kafa sun taimaka wa Adani haɓaka kasuwancinsa. Kamfanonin Adani ne suka gina wasu manyan ayyukan gwamnatin Modi a Gujrat," in ji Mista Crabtree.

A 2012, mai binciken kuɗi na gwamnatin Indiya ya zargi Mista Modi, lokacin yana ministan Gujtrat, da sayar wa Adani mai da araha daga kamfanin gwamnati da sauran 'yan kasuwa.

Wani ɗan jarida ya rubuta jerin maƙaloli a 2017, yana mai cewa kamfanonin Adani sun samu garaɓasa a gwamnatin Modi.