Shugaba Xi zai gana da Putin a Moscow a makon gobe

Asalin hoton, Reuters
A mako mai zuwa ne shugaban China Xi Jinping zai tafi Moscow domin tattaunawa da shugaban Rasha Vladimir Putin, in ji hukumomi.
Fadar Kremlin ta ce za su tattauna "daki-daki kan yadda za su haɗa hannu da kuma dabarun aiki tsakaninsu”.
Ziyarar na zuwa ne dai-dai lokacin da Beijing da ƙawarta Rasha suka yi tayin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine, wadda ƙasashen yamma za su yi maraba da ita.
Kasashen yamma sun ja kunnen Beijing kan taimaka wa Moscow da makamai.
Wannan ita ce ziyarar shugaba Xi ta farko zuwa Rasha tun lokacin da sojinta suka fara mamaya a Ukraine.
An tsara za su haɗu da shugaba Putin ranar Litinin sannan su tattauna a ranar Talata.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ya ce China za ta “kasance a tsakiya sannan ta zama ‘yar baruwana” a rikicin na Ukraine, za kuma ta taka rawar gani domin taimakawa wajen tattaunawar zaman lafiya”.
Mai magana da yawun Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak ya ce, China na taka rawar gani wajen tabbatar da Ukraine ta samu ‘yancinta, kuma suna maraba da hakan.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tabbacin da aka samu kan cewa Shugaban China zai je Rasha wata alama ce da ke nuni da goyon bayan China ga Rasha.
Babu wani abun mamaki kan hakan: Putin da Xi kallo guda suke yi wa lamuran duniya, duka suna da tunanin ganin kasashen duniya na da ra’ayoyin kansu.
A bara duka shugabannin biyu sun nuna alaƙar da ke tsakaninsu ba ta da iyaka. Kuma wannan ba gaskiya ba ne.
Har zuwa yanzu China ba ta taimakawa Rasha da ko kwayar harsashi ba domin ta samu nasara a yaƙin da take yi da Ukraine, ko da yake Amurka ta ce China na da shirin yin hakan.
Yayin da ƙasashen biyu suke ci gaba da bayyana alaƙar da ke tsakaninsu – China ta kwana da sanin Rasha ta ninkata karfin tattalin arziki – wanda hakan na nufin China ce ke a ƙasa Rasha a sama.
Gwamnatin China na da ƙarfin faɗa kan Rasha. Wani abu kuma da ke ƙara zama a gaban muradi shi ne iƙirarin Beijing na cewa ita ‘yar baruwana ce.
China ta taka muhimmiyar rawa wajen sasanta abokan gaba da ke gabas ta tsakiya, Iran da Saudiyya domin su dawo da hulɗar diflomasiyya tsakaninsu.
Ƙoƙarin China na samar da yarjejeniyar zaman lafiya da kuma mutunta ‘yancin ƙasar Ukraine abu ne mai kyau.
A watan Fabirairu, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ya so ya haɗu da Mista Xi – “Na yi imanin cewa China ba za ta bai wa Rasha makamai ba,” in ji shi.
Wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka, sun ta rawaito cewa Mista Xi zai tattauna da Zelensky ta waya bayan shugaban China ya je Moscow, sai dai har yanzu babu tabbas kan hakan.
Kyiv na matukar takurawa kan a samu tattaunawa. Sai dai Ukraine ta yi amannar Shugaba Xi zai je ziyarar ne domin nunawa duniya cewa yana da alaƙa mai kyau da Rasha.
A wata tattaunawa da BBC gabanin sanar da ziyarar shugaba Xi, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya ce : “ Ba na zaton China ta kai inda take so, abin da take son taimakawa Moscow da shi na makamai. Ba na zaton ziyarar za ta samar da sakamakon zaman lafiya.... Ziyarar zuwa Rasha wani saƙo ne da ake aikawa amma ba na zaton zai haifar da sakamakon da muke tsammani cikin gaggawa.”
Wannan saƙon na nufin cewa China da Rasha na da kusanci, wanda har ya kai Shugaban China ke ziyartar takwaransa na Rasha.
“Ina ganin wannan saƙo ne ga duniya, kuma mafi mahimmanci shi ne an tura shi ga yamma, har ga waɗanda ba na yamma ba, cewa Rasha ba ita kaɗai ba ce, Rasha na tare da ita.”
Amurka ta matsu taga tattaunawa tsakanin Mr Xi da Zelensky.
A ranar Alhamis kakakin ma’aikatar harkokin wajen China ya shawarci Kyiv da Moscow da su sabunta tattaunawar zaman lafiyar da ke tsakaninsu yayin wata tattaunawa da suka yi da Mista Kuleba.










