Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manufa da nadama kan "sauya wa mutane tunani" bayan juyin-juya-halin Iran
- Marubuci, Ali Hamedani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
- An wallafa
A yayin da Iran ke cika shekara 45 da juyin juya halin ƙasar, al'ummar da suka yi gwagwarmayar kawo sauyi a shekara ta 1979 suna ta bayyana ra'ayoyinsu.
Yayin da wasu ke nadama, wasu kuma sun kafe cewa hakan shi ne abin da ya dace.
"Shekara 45 da suka gabata, babu ɗaya daga cikin waɗanda suka yi juyin juya hali da zai yi tunanin cewa, akwai wata rana da za ta zo, mutane su yi musu kallon masu laifi," in ji Sadegh Zibakalam.
Yana daya daga cikin miliyoyin Iraniyawa da suka fito kan titunan ƙasar domin nuna adawa da Shah a lokacin juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979.
Amma a yanzu, da ake cika shekaru 45, matasan ƙasar da dama na aza ayar tambaya ga shugabannin Iran, da juyin juya halin da waɗanda suka goyi bayansa.
Mutuwar Mahsa Amini mai shekara 22 a shekarar 2022, bayan da 'yan sanda suka tsare ta, ya haddasa gagarumar zanga-zanga a faɗin ƙasar.
A cikin 2022 mutuwar Mahsa Amini mai shekaru 22, bayan da 'yan sanda masu da'a suka tsare ta, ya haifar da zanga-zangar adawa da gwamnati.
Cin zarafin bil adama, tauye yancin walwala da yanayin tattalin arzikin Iran na daga cikin abubuwan da suka haddasa rashin gamsuwa, sannan takunkuman da ƙasashen Yamma suka ƙaƙaba kan ayyukan nukiliyar Iran ya ƙara dagula lamura a ƙasar, sannan kuma hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 43 cikin 100 cikin watanni 12 zuwa Janairu.
Haka kuma hare-haren da Amurka ke kai wa ƙungiyoyin da Iran ke marawa baya a yankin.
Wasu daga cikin matasa masu tasowa sun zargi masu juyin juya hali a kan tafarkin da Iran ta dauka tare da aza ayara tambayar cewa shin da gaske wanan shi ne abin da suka yi yaƙi domin sa?
"Ba wai don son rai, ko kuma kiyayya, ko kuma girman kai da son zuciya ba, amma idan da za a koma 1979, zan sake shiga cikin juyin juya hali," in ji Zibakalam, wanda ya ce " ya shafe shekarunsa na jami'a a Birtaniya.
“Me muke so, muna son a gudanar da sahihin zabe cikin ‘yanci, ba ma son fursunonin siyasa, kuma muna son wanda zai jagoranci ƙasar nan ba tare da yin abin da ya ga dama ba.
Ya kuma ya dora alhakin matsalolin da kasar ke fama da su a kan shugabannin Iran, ba wai juyin juya hali ba.
"Kuskuren da ni da mutane irina suka yi shi ne, maimakon mu ci gaba da manufofin juyin juya halin, wato 'yanci da dimokuradiyya, sai muka biye wa taken nuna adawa da mulkin kama-karya kamar 'ganin bayan Amurka' da 'Ganin bayan Isra'ila' da 'Za mu wargaza Isra'ila."
Ya ce har yanzu yana da yaƙini kan ƙa'idojin da ya yi yaƙi kansu a shekarun 1970. A shekarar da ta gabata ya rasa aikinsa na koyar da kimiyyar siyasa a jami'ar Tehran bayan zanga-zangar nuna adawa da zalunci a ƙasar mai taken 'Mace Rayuwa 'Yanci".
Ya yi bayanin cewa shekara 45 da suka gabata, 'yanci shi ne abin da Ayatullah Ruhollah Khomeini - wanda shi ne ya kafa jamhuriyar Musulunci ta Iran - ya sha yin alƙawari da 'yan uwansa 'yan juyin juya hali.
"'Yanci haƙƙin jama'a ne. 'Yancin kasa haƙƙin kowa ne, kada su ɗaure mutum sannan a hana shi faɗin albarkacin bakinsa," in ji Khomeini a wani jawabi da ya yi a lokacin da yake zaman gudun hijira a Faransa a shekara ta 1978.
Sauraron waɗannan jawabai a yanzu ya sa mutane da yawa, musamman mutanen da ba su san lokacin mulkin Khumainia, na tunanin cewa fafutika da ake yi yanzu tsakanin 'yan gwagwarmaya da yadda ake yanzu.
Rawar da Shah da Khomeini suka taka a juyin juya halin
Mohammad Reza Pahlavi ya shafe shekara 37 a kan karagar sarautar Iran, kuma a lokacinsa ne ƙasar ta fuskanci zuwan Turawan Yamma, da ci gaban tattalin arziki, da kuma ƙoƙarin sanya kishi ƙasa a cikin al'adun gargajiya na Iran da tarihin jahiliyya.
Mata sun sami 'yancin kaɗa ƙuri'a a shekarun 1960 kuma sun sami 'yancin daidaito tsakaninsu da maza.
Birnin Tehran ya kasance birnin bukukuwan fati, inda ake samun kulub-kulob da ke shagulgula cikin dare sanna ƙasar ta riƙa fitar da barasa zuwa duniya.
Amma duk da wannan yancin walwala na zamantakewa, Shah ya fuskanci suka kan salon mulkinsa na mulkin kama karya da kuma rashin tsarin dimokuradiyya.
Malaman addinin Musulunci na Shi'a sun sha sukar sa da cewa yana tauye martabar Musulunci, yayin da ƙungiyoyin 'yan ra'ayin gurguzu da makwabciyar Iran, wato tsohuwar daular Rasha ke tasiri a kansu, suka yi kira da a samar da daidaito a tsakanin 'yan ƙasar.
Khomeini ya bayyana kansa a matsayin jigon hadin kan bangarori daban-daban na gwamnatin Musulunci.
Miliyoyin mutane na girmama shi a matsayin mutum mai tsarki da ke ƙoƙarin canza Iran zuwa al'ummar Musulunci da aka yi bayaninsu cikin littafin Kur'ani mai tsarki.
Khumaini ya samu laƙabin 'Imam', wato shugaban al'ummar musulmi.
Rahotonnin gidajen talbijin a shekarun 1979 sun nuna miliyoyin mutane cike da shauki sun jeru a kan titunan birnin Tehran a lokacin da suke tarbar Khomeini lokacin da ya koma Iran bayan zaman gudun hijira na shekara 15.
Bidiyoyin sun nuna yadda mutane suka kewaye motarsa suna ta jefa ƙwallaye da nufin sanya albarka.
Kafin komawarsa, jita-jita ta cika ƙasar cewa idan aka kalli sararin samaniyar ƙasar cikin dare da misalin ƙafe 10:00 na dare a wasu keɓantattun ranaku, za su ga fuskar Khomeini a cikin wata, a matsayin wata alama ta nasara. Da yawa sun yarda da hakan.
"Mun kaɗu, muna ta tambayar kawunanmu kan abin da ya sa mutane suka amince da waɗannan abubuwa?" in ji Farah Pahlavi, tsohowar basarakiya a Iran, wadda a yanzu ke zaman gudun hijira.
Tare da mijinta Shah da 'ya'yansu uku, ta fice daga Iran a farkon shekarar 1979 don "hutu" amma ba ta koma ba.
Shahran Tabari na ɗaya daga cikin masu ra'ayin sauyi da ƙungiyoyin da ke adawa da musulunci da suka goyi bayan Khomeini- wanda a yanzu ke zaune a birnin London.
Tana aza aya tambaya kan matakin da ya sa aka kifar da Shah ''Ba mu san me dimokradiyya ta kunsa ba'', ta ƙara da cewa wasu jam'iyyun adawa ba su goyi bayan matakin ba, amma sun yi shiru da bakinsu.
"Kowa na son Shah ya sauya ta kowane hali," in ji ta. "abu ne mai wahala a iya gano haƙiƙanin abin da ya faru. Abin ya yi kama da sauya tunani da jirkita abubuwa.
Rawar da marubuta suka taka
Farfesa Homa Nategh da ke koyarwa a jami'ar Tehran a lokacin juyin-juya halin na ɗaya daga cikin masu ra'ayi iri ɗaya da na Shahran Tabari.
Nategh - wadda ta mutu a shekarar 2016 - tana ji a ranta cewa kamar tana da laifi.
A matsayin fitacciyar 'yar gwagwarmayar masu ra'ayin kawo sauyi, ta fassara maƙaloli daban-daban tare da rubuta littattafan da suka goyi bayan matakin.
Watanni ƙalilan bayan fara mulkin masu juyin-juya-halin, sai Nategh ta fara samun saɓani da jagororin addinin, lamarin da ya sa fice daga ƙasar zuwa Faransa, inda ta ci gaba da aikinta.
A daidai wannan lokacin, ta yi hirarraki masu yawa da BBC, ta amince cewa ayyukanta sun taka rawa wajen kawar da gwamnatin Shah, ta kuma ce a yanzu tana nadamar abubuwan da ta rubuta a shekarun 1970.
Amma Sadegh Zibakalam ya musanta ra'ayin cewa an yi amfani da mutanen da aka sauya musu tunani.
"Ba haka ba ne kwata-kwata. Kalli abin da ya faru," in ji shi. "Ba za ku iya cewa dukkansu ba su da labari, su wane ne masu juyin juya hali? Dalibai ne kuma malaman jami'a, rashin ɗa'a ne a ce farfaganda ce ta yi tasiri a kansu."
Ko da yake bayan juyin juya halin, an haramta ƙungiyoyin 'yan gurguzu daban-daban, an kashe mambobinsu tare da wasu fitattun masu fafutukar juyin juya hali da suka taimaka wa Khomeini wajen kafa Jamhuriyar Musulunci, amma yana ganin sukar "sun samo asali ne daga rashin gamsuwar mutane da gwamnati mai ci".
Shugabannin Iran sun ce juyin juya halin ya 'yantar da Iran daga mamayar ƙasashen waje, musamman Amurka da ƙasashen yamma. Sun yi nuni ga dakarun juyin juya halin Musulunci (IRGC) da kafa masana'antar kera makamai ta ƙasa a matsayin shaida na dogaro da kai. Kuma sun ɗauki nauyin inganta harkar lafiya da ilimi, musamman ga talakawa.
"Ba na son abin da zai ɓata min rai"
To amma bayan shekaru arba'in bayan juyin juya halin da ya kawo ƙarshen mulkin Pahlawi, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fuskanci wata sabuwar matsala yayin da wasu masu zanga-zangar suka yi ta rera taken nuna goyon baya ga sarakunan Pahlawi.
Har ila yau, wasu tsoffin masu neman sauyi sun nemi afuwarsu.
"Abin farin ciki ne sosai cewa mutane a yanzu, duk da farfaganda na shekaru, sun fahimci abin da sarki ya yi wa Iran," in ji tsohuwar Sarauniya Farah Pahlavi. "Da yawa sun tura min saƙonin imel cewa sun shiga juyin juya hali amma yanzu sun yi nadama, suna neman afuwata."
"Zaka iya?" Ina tambaya.
"I mana!" in ji ta. "Saboda bana son abin da zai ɓata min rai."