Arsenal ta dauki Fabio Vieira daga FC Porto

An wallafa

Arsenal ta kammala cinikin Fabio Viera daga FC Porto kan yarjeniyar da zai dade yana buga wasa a Emirates.

Mai shekara 22, ya yi wa kungiyar Porto wasa 54, wadda ya fara tamaula a ciki tun daga matashin dan kwallo.

Ya fara yi wa kungiyar wasa a Yunin 2020, yana cikin wadanda suka lashe babbar gasar tamaula ta Portugal a kakar 2019/20 da kuma 2021/22.

Fabio mai buga wa tawagar Portugal tamaula ta ‘yan kasa da shekara 21 ya ci kwallo 13 a wasa 21.

Ya kuma wakilci kasarsa a gasar matasa da Portugal ta yi ta biyu a wasannin nahiyar Turai ta matasa ‘yan kasa da shekara 19 a 2019.

A kakar da aka kammala a babbar gasar Portugal, Fabio ya yi karawa 27 da cin kwallo shida da bayar da 14 aka zura a raga, inda Porto ta lashe kofin Primeira Liga.

Fabio zai saka riga mai lamba 21 daga baya zai hadu da sauran ‘yan wasan Gunners kan shirye-shiryen atisayen kakar da za a fara a cikin watan Agusta.