Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Koulibaly ya kai Senegal zagaye na biyu a Kofin Duniya a Qatar
Kalidou Koulibaly ya kai Senegal zagaye na biyu a Gasar Kofin Duniya, bayan cin Ecuador 2-1 a wasa na uku a rukunin farko da suka kara ranar Talata.
Dukkan kwallo ukun da aka zura a raga masu taka leda a Ingila ne suka ci a fafatawar da aka yi a filin wasa na Khalifa International Stadium.
Senegal ce ta fara cin kwallo a bugun fenariti ta hannun Ismaila Sarr mai taka leda a Watford daga baya Moises Caicedo mai wasa a Brighton ya farke.
Senegal ta kara na biyu ta hannun mai tsaron bayan Chelsea, Koulibally, hakan ya sa Senegal mai rike da kofin Afirka ta kai zagaye na biyu kenan.
Tun farko Ecuador ta bukaci maki daya, domin ta kai zagayen gaba kenan ko canjaras ko kunnen doki take bukata, amma hakan bai samu ba.
Daya wasan rukunin farko tsakanin Netherlands da Qatar mai masaukin baki, an ci Qatar 2-0.
Kenan Netherlands ce ta daya da maki bakwai a rukunin farko, sannan Senegal da maki shida, sai Ecuador mai maki hudu.
Qatar mai masaukin baki ta zama ta farko da ta kasa cin wasan farko, haka kuma ta kasa nasara a karawa uku a cikin rukuni a matsayin mai shirya wasan.
Da wannan sakamakon Senegal wadda ta yi ta biyu a rukunin farko za ta fafata a wasan zagaye na biyu da duk wadda ta yi ta daya a rukuni na biyu da ya kunshi Ingila da Iran da Amurka da kuwa Wales.