Damar Real ta daukar La Liga na kara dusashewa a bana

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta je ta tashi 0-0 a gidan Real Betis a wasan mako na 24 a gasar La Liga ranar Lahadi.
Wasa na biyar da kungiyar Santiago Bernabeu ta tashi canjaras a kakar nan, wadda ta ci fafatawa 16 aka doke ta uku, mai maki 53.
Hakan ya sa Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki tara tsakaninta da Barcelona ta daya.
Tun farko Barcelona ta doke Valencia 1-0 a Camp Nou ranar Lahadi a wasan babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona ta hada maki 62, wadda ta ci karawa 20 da canjaras biyu aka doke ta karo biyu.
Wadanda suka yi nasara a kan Barca a kakar nan sun hada da Real Madrid da kuma Almeria.
Real Madrid za ta karbi bakuncin Espanyol a wasan mako na 25 a gasar La Liga ranar Asabar 11 ga watan Maris..
Ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Athletic Bilbao a ranar Lahadi 12 ga watan Maris.
Rabon da Barcelona ta dauki la Liga tun bayan 2018/19 mai 26 jimilla, Real mai rike da kofin bara tana da 35, ita ce kan gaba a yawan daukar kofin a Sifaniya.










