Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zakuna biyar sun tsere daga gidan adana dabbobi a Australiya
An ƙaddamar da neman wasu zakuna biyar da suka tsere daga wani gidan adana namun daji a ƙasar Australiya.
An hangi dabbobin - waɗanda suka haɗa da babba ɗaya tare da ƙanana huɗu - ranar Laraba da sassafe a kusa da gidan adana dabbobin na Taronga da ke birnin Sydney.
Mai magana da yawun gidan namun dajin ya ce an rufe gidan dabbobin, domin kwantar wa da mutane hankali, kuma ya ce an samu nasarar mayar da dabbobin cikin ƙanƙanin lokaci.
Kawo yanzu ba a yi bayanin yadda zakunan suka fice daga gidan namun dajin ba.
Sai dai shugaban gidan dabbobin, Simon Duffy, ya kira lamarin da cewa ''al'amari ne mai muhimmanci'' da za a binciki musabbabinsa.
Ya shaida wa kafar yada labaran kasar cewa zakunan sun shiga wani ƙaramin wurin da baƙi ke zama mai tazarar mita 100 daga gidan namun dajin.
Mista Duffy ya ƙara da cewa ƙaramin wurin, wanda aka zagaye shi da katanga mai tsayin kafa shida, da ake amfani da shi domin kare mutane daga harin dabbobin da ke cikin gidan, kuma an kewaye ilahirin gidan da doguwar katanga.
Mista Duffy ya ce bidiyo da kyamarorin tsaro suka ɗauka sun nuna yadda mai gadin gidan ya ankarar da mutane minti 10 bayan tserewar zakunan.
Ya ƙara da cewa nan take ma'aikatan gidan suka fito domin taimaka wa mutanen da ke harabar gidan tseretar da rayuwarsu.
An samu nasarar mayar da huɗu daga cikin zakuna inda ake tsare da su 'cikin kwanciyar hankali'.
Wajen ajiye zakunan zai ci gaba da kasancewa a rufe har zai an yi gyare-gyare domin tabbatar da cewa babu wata barazana, kamar yadda Mista Duffy ya bayyana.
Ba kasafai ake samun labaran tserewar dabbobi a gidajen namun dajin Australiya ba.
A shekarar 2009, wata zakanya ta fice daga wajen da take ajiye a gidan namun dajin Mogo, da ke kudancin birnin Sydney, kuma dole aka kasheta ta hanyar harbi saboda hatsarin da za ta iya haifar wa mutane.