Ba zan aske gashin kai na ba in ji Cucurella

An wallafa

Dan kwallon Chelsea, Marc Cucurella ya ce ba zai aske gashin kansa ba - duk da cewar sumar ta taka rawar da Tottenham ta farke kwallo a Stamford Bridge.

Cristian Romero ya ja gashin kan mai tsaron bayan da ta kai an kai shi kasa a wasan Premier League da suka fafata ranar Lahadi.

Ba a dauki wani hukunci ba, bayan da na'urar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato VAR ta yi nazarin abin da ya faru.

Harry Kane ne ya farke kwallo na biyu da Chelsea ta tashi 2-2 a wasan na hamayya daf da za a tashi.

Sai dai Cucurella ya ce: ''Ba zan taba aske gashin kai na ba. Wannan shi ne salo na.''

Chelsea ta dauki mai tsaron bayan daga Brighton kan fam miliyan 60 a bana, wanda ya sa hannu kan yarjejeniyar kaka shida.

Cucurella ya ce wannan kwantiragin za ta amfane shi a cikin fili.

Mai shekara 24 ya ce ''Yarjejeniyar da na amince tana da tsawo, amma hakan zai taimakamin na nuna kwarewar da nake da ita a kungiyar.

Kociyan Chelsea, Thomas Tuchel ya dade yana bibiyar Cucurella, tun lokacin da yake makarantar koyon tamaula a Barcelona.