Ashe kasa rabuwa da tarkacen kayayyaki larura ce?

Kofunan shayi, kwalaben da ba komai a ciki, 'yar tsana, robobin zuba abinci, kasa-kasan CD...ana iya samun kusan komai a gidan Edward Brown.
An ɗoɗɗora kayayyakin wani kan wani ba tare da tsari ba, kuma hakan ya sa kayayyakin sun mayar da gidan Brown wuri mai wuyar zama.
"Babu wurin da mutum zai yawata idan ya shigo nan," a cewar mutumin mai shekara 60 mazaunin Blackbuurn da ke arewacin Ingila.
"Shi kansa ya fuskanci yana da matsala.
Yana fama ne da larurar da ake kira "ɓoye kayayyaki", wata lalurar ƙwaƙwalwa da ke sa masu fama da ita su kasa rabuwa da wani abu da ba shi da muhimmanci.
"Wannan matsala kan jawo cushe-cushen abubuwa da ke hana yin zirga-zirga," in ji Gregory Chasson, wani likitan ƙwaƙwalwa kuma mai shirin zama farfesa a Cibiyar Fasaha ta Illinois da ke Amurka.
"Ba za a iya amfani da ɗakuna ba saboda abin da aka gina su don shi: ba za ka iya amfani da kicin ba don yin girki ko kuma amfani da ɗaki don yin barci," kamar yadda Brown ya faɗa wa BBC.
Kayayyaki irinsu takardun jarida, da mujalloli, da robobin zuba abinci, da takalma, da wayoyi, da lema, da murafen kwalaba - kayayyakin da ke da kyau da waɗanda suka tsufa - kan zama masu kyau a idon mai wannan larurar.
Ɓoye kaya bai keɓanci wani jinsi ba ko al'ada.
Yakan shafi kashi 2.5 cikin 100 na al'ummar duniya da ke da shekarun haihuwa 60, da kuma waɗanda ke da larurar tsananin damuwa ko zaƙuwa, kamar yadda ƙungiyar Kula da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa ta Amurka ta bayyana.
Wani bincike da aka wallafa a mujallar Journal of Psychiatric Research a watan Disamban 2021 ya ce alamomin matsalar "sun ƙaru sosai" a lokacin annobar korona.
Jin kusanci da abu

Asalin hoton, Getty Images
Wata alama mai muhimmanci kan masu oye kayayyakin ita ce yadda suke jin wata buƙata mai ƙarfi ta ci gaba da riƙe kayayyaki.
"Mutane na son su ci gaba da riƙe kayan ne saboda imanin da suke da shi kansu da kuma sha'awar da suke da ita na mallakar abin," kamar yadda Christiana Bratiotis ta yi bayani.
Bratiotis ta ce wasu daga cikin magabatanta kan ce "wannan rukunin kayan na da muhimmanci a wajena da 'yar uwata, idan na rabu da su kamar na rabu da ita ne".
Haka nan, masu wannan lalura na jin cewa wata rana za su buƙaci kayan.
Illar ƙin rabuwa da tarkacen kaya
Akwai illoli da dama game da ƙin rabuwa da kayayyaki - kuma suna da girma fiye da yaddda mutane ke tunani.
Idan muka fara da na bayyane, "Ɓoyewa ko ƙin rabuwa da kayayyaki ka iya jawo dukkan illoli: kamar gobara, da tuntuɓe, da jin rauni, da kuma haɗarin kamuwa da cutukan nimfashi kamar asthma," in ji Gregory Chasson.
Game da larurar ƙwaƙwalwa kuma, hakan kan sa mai fama da matsalar ya zama saniyar ware a tsakanin al'umma.
"Sukan ɓoye wani yanayi a tare da su da ba sa so mutane su gani saboda gudun tsangwama, wanda mutanen ke kallo a matsayin lalaci, ko rashin tarbiyya, ko rashin tsari, kuma ba sa kallon hakan a matsayin lalurar ƙwaƙwalwa," a cewar Bratiotis.
Wane ne mai ƙin rabuwa da kayayyaki?

Asalin hoton, Getty Images
Da yawa daga cikinmu kan ajiye abubuwa bisa dalilai daban-daban. Hasali ma, idan ana maganar halayenmu na yau da kullum, mu masu farauta ne da ke yayumo abubuwa don mu ajiye su a tsawon rayuwarmu.
Sai dai ba lallai ne hakan na nufin muna da matsalar ɓoye kayayyaki ba.
Bratiotis ta yi bayanin cewa ɓoyewa ko ƙin rabuwa da kayayyaki ɗabi'a ce "kuma takan girma daga ƙarama zuwa babba". Amma yaushe ne muke gane mutum mai ɓoye abubuwa?
"Wani zubin abu ne mai wuya a gane kai-tsaye," a a cewar Chasson. "Amma yakan zama matsala wadda kuma za a iya ganowa idan ta fara haifar wa mutum da damuwa gare su ko kuma kan waɗanda ke tare da su."
Idan kuna tunanin ɓoye kayayyaki, babu mamaki kun taɓa tunanin wani mutum da gidansa ke maƙare da kaya barkatai har ma suna hana shi zirga-zirga.
Waɗannan lamurra ne da suka tsananta. Don gane yadda ɓoye kayayyaki ke zama larura, ku duba hoton da ke ƙasa:

Asalin hoton, Getty Images
Abin da ke haifar da larurar
Tara kayayyakin wata alama ce kawai ta fili da ake gani.
"Amma tarin kayayyakin na nuna wata matsala da ba a gani amma kuma su ne ke taruwa su haifar da irin wannan larurar," a cewar Bratiotis.
Akwai abubuwa game da rayuwar mutum - kamar shan wahala wajen yanke hukunci, tunanin kyautata komai, da kuma inda-inda - waɗanda su ne suke taruwa su haifar wa mutum larurar kasa rabuwa da tarkace.
Maganin larurar

Asalin hoton, Getty Images
Ya zuwa yanzu, babu wani magani da ake bayarwa saboda matsalar kasa rabuwa da tarkace. Amma hanyar maganinta shi ne samun shawarwarin ƙwararru game da tunanin mai fama da larurar - wanda ake kira Cognitive-Behavioural Therapy (CBT) a turance.
Amfanin CBT shi ne sauya tunanin mutane don sauya ɗabi'arsu da kuma kyautata tunaninsu.
"Sakamakon da ake samu ba yabo ba fallasa. Ba za a ce ba shi da amfani ba, amma kuma ba ya magani nan take," in ji Bratiotis.











