Abinda kuke son sani kan wasan Real Madrid da Atalanta

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na fatan lashe Uefa Super Cup na shida jimilla, wadda za ta fafata da Atalanta a National Stadium a birnin Warsaw a Poland ranar Laraba.
Kawo yanzu Real ta yi kan-kan-kan da Barcelona ta Sifaniya da AC Milan masu biyar-biyar a tarihi.
Ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta buga wasan ne, bayan da ta doke Borussia Dortmund 2-0 a Wembley ta lashe Champions League a bara.
Kofi na 13 da Ancelotti ya ɗauka kenan jimilla a matakin mai horar da Real Madrid, idan kuma ya lashe Uefa Super Cup na bana zai ɗauki na 14 irin bajinyar na Miguel Munoz ya yi a ƙungiyar.
Haka kuma da zarar Ancelotti ya yi nasarar lashe kofin nan, zai zama na huɗu kenan, zai haura Pep Guardiola mai uku a yawan ɗaukar kofin a tarihi.
Real ta taka rawar gani a 2023/24, wadda aka kasa doke ta a wasa 26 a dukkan karawa mai nasara 17 da canjaras tara.

Asalin hoton, Getty Images
Kakar da ta taka rawar gani kenan tun bayan bajintar Janairun 2017 karkashin Zinedine Zidane, wadda ta yi karawa 40 da cin 30 da canajaras 10,
Real Madrid ta ɗauki Kylian Mbappe a bana don kara karfin ƙungiyar, kuma zai buga wasan na Uefa Super Cup ranar Laraba.
Rabonda ɗan wasa ya ci wa Real ƙwallo a karawarsa ta farko tun Jude Bellingham a wasan La Liga da Athletic Club a Agustan 2023.
Mbappe ya ci ƙwallo shida a wasan karshe a ƙungiyarsa ta baya da tawagar Faransa da ya haɗa da ɗaya a Coupe de France a 2021 da ɗaya a UEFA Nations League a 2021 da uku a wasan karshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022 da ɗaya a Trophée des Champions a 2021 Paris St Germain.
Ana sa ran ɗan kasar Brazil, Vinicius Junior zai taka rawar gani a wasan, wanda yake da hannu a cin ƙwallo 10 a wasan karshe 10 a Real Madrid, wanda ya ci bakwai ya bayar da uku aka zura a raga.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shi ne karon farko da Atalanta za ta kara a Uefa Super Cup, wadda ta ɗauki Europa League, bayan cin Bayer Leverkusen 3-0 a watan Mayu.
Shi ne babban kofi da ƙungiyar ta ɗauka, bayan da ɗan Najeriya, Ademola Lookman ya ci uku rigis a wasan karshen - shi ne na shida da ya yi wannan bajintar a wasan karshe a gasar Uefa.
Kociyan Atalanta, Gian Piero Gasperini ya zama na huɗu mai yawan shekarun haihuwa da ya lashe kofin zakarun Turai a tarihi mai shekara 66 da kwana 117 a lokacin.
Sauran sun haɗa da Raymond Goethals mai shekara 71 da kwana 231, wanda ya lashe UEFA Champions League a 1993 da Jupp Heynckes mai shekara 68 da kwana 16, wanda ya ɗauki UEFA Champions League a 2013 da Sir, Alex Ferguson mai shekara 66 da kwana 142, wanda ya lashe UEFA Champions League a 2008.

Asalin hoton, Getty Images
Europa League shi ne kofin da Atalanta ta ɗauka bayan wasa huɗu na karshe da Gasperini ya ja ragamar ƙungiyar, bayan rashin nasara karo uku a Coppa Italia tare da shi.
Atalanta ta fitar da makudan kuɗi ta sayi ƴan wasa a bana da ya haɗa da Charles De Ketelaere daga AC Milan – wanda ya ci ƙwallo 14 a wasannin aron da ya buga mata a bara – ta kuma ɗauki Mateo Retegui daga Genoa, wadda jimilla ta biya £48m.
Wannan shi ne karo na uku da Real Madrid za ta fafata da Atalanta, bayan da suka kara a Champions League a zagayen ƴan 16 a 2020/21.
Real ce ta yi nasara a karawar biyu, wadda ta fara cin 1-0 a Bergamo da kuma cin 3-0 a Alfredo Di Stéfano Stadium.
A kakar ce Real ta kai daf da karshe a gasar daga baya Chelsea ta yi waje da ita, bayan nasara gida da waje.
Wasan karshe da aka fafata a Uefa Super Cup tsakanin ƙungiyar Sifaniya da ta Italiya, shi ne a 2010, inda Atletico Madrid ta doke Inter Milan 2-0 a Monaco.









