Ko Man United ta zama kayan ruwa ne? - 'Komai ya yi wuya a kulob ɗin'

Kocin Manchester United Ruben Amorim

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasa biyu kacal Manchester United ta ci cikin shida da ta buga a gasar Premier League ƙarƙashin sabon koci Ruben Amorim
    • Marubuci, Simon Stone at Old Trafford
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief football news reporter
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Anya al'amura za su lalace wa Manchester United fiye da yadda suke a yanzu?

A ranar Lahadi Bournemouth ta casa United 3-0 har gida a wasan Premier League, sannan Tottenham ta cinye ta 4-3 ranar Alhamis a gasar Carabao Cup.

Sakamakon na ranar Lahadi na nufin Machester ƙauyen za ta ƙare bikin Kirsimeti a mataki na 13 a teburin Premier, kuma wannan ne karon farko da take zaune a matakin goman ƙarshe tun kafin a raɗa wa gasar sunan Premier League.

Magoya baya - waɗanda suka yi wa sabon koci Ruben Amorim ihu bayan tashi daga wasan - ransu ya ɓaci sosai game da ƙarin kuɗin tikitin shiga kallon wasan zuwa fam 66.

Tuni suka bayyana cewa za su haɗa gwiwa da magoya bayan Liverpool wajen yin zanga-zanga idan suka haɗu a filin wasa na Anfield ranar 5 ga watan Janairu mai zuwa.

Yayin da Amorim ke faɗa wa manema labarai cewa yana ganin magoya bayan sun gaji da abubuwan da suke gani, sai ga wani ɓangare na rufin filin wasan ya rikito, abin da ya jawo ruwa ya mamaye layin gaba na ɗakin taron manema labaran.

Ɗanwasan baya Lisandro Martinez ya faɗa wa shirin BBC na Match of the Day cewa abin da yake faruwa a cikin fili na "ɓata masa rai". Sai dai kocin nasa ya ba da amsa shi ma.

"A irin wannan yanayin, komai ya lalace," in ji Amorim. A kulbo kamar Manchester UNited, idan ka sha kashi 3-0 har gida abin zai yi wa kowa wuyar fahimta.

"Tabbas magoya baya ransu a ɓace yake. Muna iya jin hakan a cikin fili. Tun bugun gida na farko da Onana zai yi, yana ta tunanin me ma zai yi, yana ta nuna wa abokan wasansa abin da ya dace su yi saboda kowa ya zaƙu.

"Na fahimci hakan, amma dai dole ne mu rungumi matsalar."

Ruben Amorim

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ruben Amorim ya kashi a wasan Premier League uku cikin shida da ya jagoranta a United zuwa yanzu

Idan akwai wani babban abu da sabon kocin ya sauya bayan karɓar ragama daga Eric ten Hagi a watan da ya gabata, shi ne yawan riƙe ƙwallo da Man United ke yi yanzu a wasanninta.

Yawan riƙe ƙwallonsu ya ƙaru da kashi 60 cikin 100 a wasan Lahadin. United ta buga jimillar shot mafi yawa kuma ta fi buga masu haɗari sama da Bournemouth. Amma duk da haka ta sha kashi, mummunan kashi.

Wannan ne karo na biyu kacal a tarihinta - na farkon shi ne a wasansu da Burnley a shekarun 1960 - da ta sha kashi sau biyu a jere a hannun kulob ɗaya da ƙwallo uku.