Lewandowski ya ci Alaves ƙwallo uku rigis a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta je ta doke Deportivo Alaves 3-0 a wasan mako na tara a La Liga da suka fafata ranar Lahadi.
Robert Lewandowski ne ya ci uku rigis a wasan, inda Raphinha ya fara bashi biyun da ya zura a raga, sannan Eric Garcia ya bashi ta ukun da ya ci.
Da wannan sakamakon Barcelona tana matakin farko da maki 24, Real Madrid ce ta biyu mai maki 21, ita kuwa Alaves mai maki 10 tana ta 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona ta fara komawa kan ganiya kenan, bayan doke ta 4-2 da Osasuna ta yi, wadda ta kawo karshen karawa bakwai da ta yi nasara a jere a La Liga a kakar nan.
Wannan shi ne karon farko da aka ci Alaves a gida a bana, wadda ta yi canjaras da Real Betis, sannan ta yi nasara a kan Las Palmas da kuma Sevilla.
Tun bayan da Barcelona ta yi rashin nasara 1-0 a Camp Nou a 2016 a hannun Alaves, daga nan ba a doke ta ba, inda take nasara gida da waje a haɗuwar da suke yi.
Rabon da Alaves ta ci Barcelona a gidanta tun 2001 a gasar La Liga.
Wasannin da aka buga tsakanin Alaves da Barcelona a bara:
La Liga Asabar 3 ga watan Fabrairu 2024
- Alaves 1 - 3 Barcelona
La Liga Lahadi 12 ga watan Nuwamba 2023
- Barcelona 2 - 1 Alaves










