'Shugaba Tinubu bai zo mulki don ƴan Najeriya su shiga wahala ba'
'Shugaba Tinubu bai zo mulki don ƴan Najeriya su shiga wahala ba'
An wallafa
Ministan Yaɗa Labarai na Najeriya Mohammed Idris ya ce manufar gwamnatin APC ita ce inganta rayuwar 'yanƙasa, yana mai cewa Bola Tinubu "bai nemi mulki don ya wahalar da 'yan Najeriya ba".
Yayin wata hira ta musamman da BBC game da cikar Najeriya shekara 64 da samun 'yancin kai, ministan ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da suka saka a gaba shi ne dawo da kishin ƙasa.



