Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United da Tottenham sun buga canjaras a Europa
Manchester United ta buga canjaras 2-2 a gidan ƙungiyar kwallon kafa ta Lyon a Faransa, a wasan zagayen kwata fayinal na ƙaramar gasar zakarun Turai ta Europa League.
Tun a minti na 26 Amada ya ci wa Lyon ƙwallo daga bugun tazara, kafin Leny Yoro ya farke ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, da kuma wadda Joshua Zirkzee ya ci a minti na 88.
Man united ta zaci ta cinye wasan amma sai Ryan Cherki ya farke kwallo ta biyun a injuri tayim.
Shi ma wasa tsakanin Tottenham da Frankfurt ya tashi 1-1, haka nan Rangers da Athletic Bilbao sun tashi babu ci, sai kuma wasan da Bodo Glimt ta ƙasar Norway ta doke Lazio ta Italiya 2-0.
Ita kuwa Chelsea na ci gaba yunƙurin lashe 'yar ƙaramar gasar zakarun Turai ta Conference League, bayan ta doke Legia Warsaw har gida da ci 3-0.
A mako mai zuwa ne za a buga falle na biyu na wasannin, ciki har da na babbar gasar ta Champions League.