Palmer ya yi bajinta a wasan da Chelsea ta caskara Aston Villa

Cole Palmer

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Cole Palmer ya taka rawar gani a wasan da Chelsea ta doke Aston Villa a Premier League ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Nicolas Jackson ne ya fara ci wa Chelsea ƙwallo a minti na bakwai da fara tamauala, sannan Enzo Fernandez ya kara na biyu kafin hutu.

Saura minti bakwai a tashi daga karawar Cole Palmer ya ci na uku, kuma na takwas da ya ci a bana a Premier League, iri ɗaya da yawan na Jackson a kakar nan.

Kenan Aston Villa ta yi wasa takwas a jere ba tare da nasara ba a dukkan fafatawa, wadda ta yi canjaras uku aka doke ta wasa biyar.

Tun bayan da Villa ta doke Bologna 2-0 a Champions League ranar 22 ga watan Oktoba, daga nan ta ci karo da koma baya.

Wannan shi ne karon farko da Unai Emery ya ja ragamar wasa da yawa a jere ba tare da yin nasara ba.

Tun bayan da Villa ta doke Bologna 2-0 a Champions League ranar 22 ga watan Oktoba, daga nan ta tashi 1-1 da Bournemouth a Premier, sai Crystal Palace ta fitar da ita daga League Cup da cin 2-1.

Villa ta yi rashin nasara 4-1 a gidan Tottenham a Premier, sannan Club Brugge ya doke Villa 1-0 a Champions League.

Haka kuma Villa ta je ta kwaso ƙwallo 2-0 a gidan Liverpool a Premier daga nan ta tashi 2-2 da Crystal Palace a Premier a Villa Park.

Aston Villa ta tashi 0-0 da Juventus a gasar zakarun Turai da kuma wanda Chelsea ta doke ta 3-0 ranar Lahadi a Stanford Bridge a Premier.

Chelsea ta yi sama zuwa mataki na uku a teburin Premier League da maki 25, iri ɗaya da na Arsenal ta biyu.

Ranar Asabar Arsenal ta je ta ɗura 5-2 a West Ham a fafatawar mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Ranar Laraba, Chelsea za ta je gidan Southampton a karawar mako na 14 a Premier, yayin da a ranar ce Aston Villa za ta karɓi bakuncin Brentford.