Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ko Man United ta yi zaɓen tumun dare?
Har yanzu Manchester United ba ta kamo bakin zari ba a wasannin da take yi, duk da daukar sabon koci Ruben Amorin daga Sporting Lisbon a cikin kakar nan.
United ta kori Erik ten Hag, sakamakon rashin kokarin da ƙungiyar ke yi, wadda ta bai wa Ruud van Nistelrooy riƙon ƙwarya
Amorim ya fara jan ragamar United ranar 11 ga watan Nuwambar 2024 da yin 1-1 da Ipswich Town a Premier League.
Kawo yanzu ya ja ragamar karawa 10 da cin wasa huɗu da canjaras ɗaya aka doke ta karo biyar.
United tana ta 14 a kasan teburin Premier League bayan karawa 18, ta yi nasara shida da canjaras huɗu aka doke ta takwas daga ciki mai maki 22.
Ɗan jarida Abubakar Sadiq daga Bauchi ya ce hakika United ta yi zaɓen tumun dare da zarar sabon kociyan bai mayar da ƙungiyar kan ganiya ba, kafin a kammala kakar bana.
Ya kara da cewar har yanzu matasan United ba su laƙanci sabon salon da Amorin ke amfani da shi ba a fannin taka leda, shi ya sa take fuskantar kalubale.
Sabon kociyan ya amince da yin amfani da ƴan wasa uku daga baya da huɗu a gabansu sai guda biyu a gaba da mai cin ƙwallo ɗaya da ake kiran salon 3-4-2-1.
Ɗan jaridan ya ce cin wasanni kan bai wa ƙungiya damar taka rawar gani a kowacce gasa, saboda haka dole Amorim ya koma lashe dukkan wasannin da zai fuskanta nan gaba.
Shi kuwa Muhammadu Sani gidan dare ɗan jarida ya ce magoya bayan United rashin hakuri ne da su, domin har yanzu kocin bai fuskanci wasu daga ƴan wasan da ya tarar ba.
Gidan Dare ya kara da cewar idan United za ta fitar da maƙudan kudi ta sayo sabbin ƴan wasa, tabbas kociyan zai iya yin abin ƙirki a ƙungiyar na gaba.
Ya kuma ce United ta yi bajinta da ta ɗauki kociyan domin matashi ne ya kuma san abinda yake yi, amma sai an yi hakuri.
To sai dai ya ce idan har kociyan bai kamo bakin zari ba, sannan ya kasa yin kokari fiye da na Ten Hag a United, tabbas ƙungiyar ta yi zaɓen tumun dare.
Sai dai Gidan dare ya ce yana da tabbacin Amorin zai mayar da United kan ganiya, amma sai an haɗa da yin haruri, kafin komai ya koma yadda ya kamata.
Ranar Litinin 30 ga watan Disamba, United za ta kara da Newcastle United a Old Trafford.
Wasa biyar da ke gaban Manchester United:
Premier League Litinin 30 ga watan Disamba
- Man Utd v Newcastle
Premier League Lahadi 5 ga watan Janairu
- Liverpool v Man Utd
English FA Cup Lahadi 12 ga watan Janairu
- Arsenal v Man Utd
Premier League Alhamis 16 ga watan Janairu
- Man Utd v Southampton
Wasa 10 da Amorim ya ja ragamar United a dukkan fafatawa:
Ranar 24 ga watan Nuwamba - Premier League
- Canjaras 1-1 da Ipswich a wasan waje
Ranar 28 ga watan Nuwamba - Europa League
- Nasara 3-2 da Bodo/Glimt a Old Trafford
Ranar 1 ga watan Disamba - Premier League
- Nasara 4-0 da Everton a Old Trafford
Ranar 4 ga watan Disamba - Premier League
- Rashin nasara 0-2 da Arsenal a wasan waje
Ranar 7 ga watan Disamba - Premier League
- Rashin nasara 2-3 da Nottingham Forest a Old Trafford
Ranar 12 ga watan Disamba - Europa League
- Nasara 2-1 da Viktoria Plzen a wasan waje
Ranar 15 ga watan Disamba - Premier League
- Nasara 2-1 da Man City a wasan waje
Ranar 19 ga watan Disamba - EFL Cup
- Rashin nasara 3-4 da Tottenham a wasan waje
Ranar 22 ga watan Nuwamba - Premier League
- Rashin nasara 0-3 da Bournemouth a Old Trafford
Ranar 26 ga wwatan Disamba - Premier League
- Rashin nasara 0-2 da Wolves a wasan waje