Harin Isra'ila ya kashe 'yanjarida uku a Lebanon

    • Marubuci, Riam El Dalati
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Lebanon
    • Marubuci, Adam Durbin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, London
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wani gida - wanda 'yanjarida ke zama a ckinsa a kudu maso gabashin Lebanon - ya kashe 'yanjarida uku, kamar yadda shaidu suka bayyana wa BBC.

An kai harin ne kan gidan saukar baƙi - wanda gomman 'yan jarida na kafofin yaɗa labarai aƙalla bakwai ke amfani da shi - a Hasbaya da ke kudancin lebanon.

Harabar gidan cike take da motocin da aka rubutawa alamar na 'yanjarida ne (Press) ƙarara a jikinsu.

'Yanjaridar uku da aka kashe ma'aikatan gidajen talbijin na Al-Manar TV da Al-Mayadeen TV ne a ƙasar, wadanda tuni suka fitar da saƙon ta'aziyya ga ma'aikatan nasu.

Ministan yaɗa labaran Lebanon ya ce da gangan aka kai harin - wanda ya bayyana da ''laifin yaƙi''.

Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba, amma a baya ta sha musanta zargin kai wa 'yanjarida hare-hare.

Mutanen sun ƙunshi mai sarrafa kyamara Ghassan Najjar, da injiniya Mohamed Reda na gidan talabijin ɗin Al Mayadeen, da kuma wani mai sarrafa kyamarar Wissam Qassem na kafar Al-Manar mai alaƙa da Hezbollah.

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce an jikkata wasu mutum uku a harin.

'Yanjarida biyar aka kashe jimilla tun bayan fara kai hare-haren Isra'ila a Lebanon, ciki har da na kamfanin labarai na Reuters Issam Abdallah.

Bidiyon da kafar Al-Jadeed TV ta wallafa - wadda ita ma 'yanjaridarta ke cikin ginin - ya nuna yadda aka ragargaza ginin da kuma rufinsa da ya da daɓensa da suka cika da ɓaragguzai.

"An faɗa wa duka ɓangarorin cewa wannan gidan na 'yanjarida ne. Mun yi magana da su duka," a cewar wani ɗanjaridar Al-Jadeed yana magana daga cikin ɓaraguzai cike da ƙura kai-tsaye.

'Yanjaridar Lebanon da ke kawo rahotonnin hare-hare a kudancin ƙasar sai da suka yi hijira daga unguwar Marj'youn zuwa Hasbaya saboda haɗarin zama a wurin.

Youmna Fawwaz, wata wakiliyar MTV Lebanon, ta faɗa wa BBC cewa hare-haren ne suka tashi 'yanjaridar daga barci da misalin ƙarfe 3:00 na dare (1:00 agogon Najeriya).

Ta ce sili ya farfaɗo musu a ka, kuma ɓaraguzai da ƙura sun lulluɓe su yayin da ake jin ƙarar jiragen sama.

"An kai harin ne da gangan. Kowa ya san muna ciki. An rubuta jarida da talabijin a duka jikin motocin, kuma ko gargaɗi ba a yi mana ba," in ji ta.

Ministan yaɗa labarai na Lebanon ya zargi Isra'ila da kai wa 'yanjarida hari da gangan, abin da ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.