Barcelona za ta yi wasa biyar ko shida cikin watan Fabrairu

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ƙungiyar Barcelona za ta yi karawa biyar a cikin kwana 20 a watan Fabrairu, guda huɗu a La Liga da zagayen kwata fainal a Copa del Rey.

To sai dai da zarar Barcelona ta yi waje da Valencia a Copa del Rey, za ta yi wasa na shida a watan, shi ne zagayen daf da karshe ranar 25/26 a Fabrairu.

Wasan farko da Alaves

A watan na Fabrairu, Barcelona za ta fara wasan La Liga a watan, inda za ta kece raini da Alaves, domin fafatawa a filinta na Olímpic.

Alaves tana mataki na 17 a kasan teburin La Liga da maki 21, Barcelona kuwa tana ta ukun teburin kakar bana.

Copa del Rey zagayen kwata fainal

Ranar Alhamis 6 ga watan Fabrairu, Barcelona za ta yi karawa ta biyu a Fabrairu, wadda za ta fuskanci Valencia a zagayen daf da na kusa da na karshe a Copa del Rey.

A bayan nan Barcelona ta caskara Valencia 7-1 a babbar gasar tamaula ta La Liga ranar 26 ga wwatan Janairu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Za kuma a bugan wasan a gidan Valencia a Mestalla.

Da zarar Barcelona ta yi nasara a karawar, za ta samu damar kai wa zagayen daf da karshe a Copa del Rey da za ta yi wasa ranar 25 ko kuma 26 ga watan Fabrairu.

Maki tara za ta yi hari

Bayan ta kammala wasan Copa del Rey da Valecia daga nan Barcelona za ta je Sevilla, domin buga La Liga ranar 9 ga watan Fabrairu.

Kwana takwas tsakani Barcelona za ta karɓi bakuncin Rayo Vallecano ranar Litinin 17 ga watan Fabrairu a La Liga a Estadi Olímpic.

Wasan karshe da Barcelona za ta yi a watan na Fabrairu, shi ne wanda za ta je Las Palmas ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu, domin buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Wasannin da Barcelona za ta buga a cikin watan Fabrairu:

Spanish Liga Ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu

  • Barcelona da Alaves

Copa del Rey Ranar Alhamis 6 ga watan Fabrairu

  • Valencia da Barcelona

Spanish Primera Liga Ranar Lahadi 9 ga watan Fabrairu

  • Sevilla da Barcelona

Spanish Liga Ranar Litinin 17 ga watan Fabrairu

  • Barcelona da Rayo Vallecano

Spanish Liga Ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu

  • Las Palmas da Barcelona