Wa zai kai wasan gaba tsakanin Real da Man City a Champions League?

Real City

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Real Madrid za ta karɓi bakuncin Manchester City a wasa na biyu a Champions League karawar cike gurbi ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Ƙungiyar Sifaniya ce ta yi nasara 3-2 a wasan farko da suuka buga a Etihad ranar Talata 11 ga watan Fabrairu.

City ta ci ƙwallo biyu ta hannun Erling Haaland, yayin da Kylian Mbappe da Brahim Diaz da Jude Bellingham suka ci wa Real Madrid ƙwallayenta.

Wasan da Real ta yi nasara a Etihad a makon jiya, shi ne na farko da ta doke City a karo na bakwai da ta kai ziyara Ingila a Champions League.

Haka kuma karo na 300 da Real Madrid ta yi nasara a dukkan gasar zakarun Turai har da European Cup da Champions League, ita ce kan gaba a wannan bajintar.

Wannan shi ne karo na 14 da za a kece raini tsakanin Real Madrid da Man City, bayan da kowacce ta yi nasara huɗu da canjaras biyar.

Real Madrid ce mai rike da Champions League da ta lashe a bara, kuma na 15 jimilla, ita kuwa City tana da guda ɗaya tal.

Carlo Ancelotti ya ce bai amince da batun Pep Guardiola cewar yana da kaso ɗaya cikin 100, idan zai kai zagayen gaba a wasan na ranar Laraba.

Kociyan City ya ce suna da jan aiki a kansu na ganin sun fitar da Real Madrid a Santiago Bernabeu, bayan rashin nasara 3-2 a Etihad a makon jiya.

Tuni mai tsaron bayan Real Madrid, Antonio Rudiger ya yi atisaye, yayin da ake fatan Federico Valverde zai murmure ya buga wasan na hamaya.

City mai Champions League da ta lashe a 2023, za ta je Sifaniya da ƙwarin gwiwa, bayan da Haaland ya yi atisaye ranar Talata, wanda ya ɗan bugu a wasa da Newcastle.

City ta caskara Newcastle United 4-0 a Premier League ranar Asabar, watakila irin salon da ƙungiyar Etihad za ta yi amfani da shi a Sifaniya ranar Laraba.

Haka kuma Ruben Dias da Nathan Ake da kuma Jack Grealish duk sun yi atisaye ranar Talata, waɗanda ba su buga karawar Premier ba ranar Asabar.

Kovacs ne raflin wasan Real Madrid da Man City

Kovacs

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, UEFA ta bayyana Istvan Kovacs a matsayin wanda zai yi rafli a wasan Real Madrid da Manchester City ranar Laraba a Sifaniya.

Kovacs ɗan kasar Romania zai busa wasan da ya haɗa da Real Madrid a gasar zakarun Turai karo na huɗu a tarihi.

Kuma karo na biyu da zai yi alkalancin karawa tsakanin Real da City, shi ne rafli a lokacin da City ta ci Real 4-3 a daf da karshe a Champions League a 2021/22.

Wasa uku da Kovacs ya busa wa Real Madrid:

Real Madrid 5-2 Borussia Dortmund Champions League league 2024/25.

Liverpool 2-5 Real Madrid Champions League 2022/23.

Manchester City 4-3 Real Madrid Champions League 2021/22.

Ƴan Real Madrid da za su fuskanci Manchester City:

Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Sergio Mestre.

Masu tsare baya: Alaba, Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Asencio.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Ceballos.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.

Ƴan Manchester City da za su kara da Real Madrid:

  • Ruben Dias
  • John Stones
  • Nathan Ake
  • Omar Marmoush
  • Mateo Kovacic
  • Erling Haaland
  • Jack Grealish
  • Jeremy Doku
  • Nico Gonzalez
  • Kevin De Bruyne
  • Stefan Ortega Moreno
  • Ilkay Gundogan
  • Bernardo Silva
  • Josko Gvardiol
  • Savinho
  • Matheus Nunes
  • Ederson
  • Scott Carson
  • Abdukodir Khusanov
  • Phil Foden
  • Rico Lewis
  • James McAtee