Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya: Kan dalilan da suka El-Rufai ya goyi bayan Tinubu a zaɓen 2023
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce yana fatan nan ba da jimawa ba manyan jagororin jam'iyyun hamayyar Najeriya za su bi shi zuwa jam'iyyar SDP da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abukar na PDP da Peter Obi na LP da sauran jiga-jigai.
Malam Nasir El Rufai ya ƙara da cewa burinsu shi ne samar da wata haɗaka kwatankwacin wadda masu hamayya suka yi a 2015 domin tunkarar jamiyya mai mulki ta APC.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Malam Nasir El-Rufa'i ya shaidawa, Usman Minjibir cewa ba ya da-na-sanin goyon bayan Bola Tinubu saboda waɗansu dalilai guda biyu.