An raba maki tsakanin Liverpool da Arsenal a Premier

Asalin hoton, Getty Images
An tashi 2-2 tsakanin Liverpool da Arsenal a wasan mako na 36 a Premier League da suka fafata a Anfield ranar Lahadi.
Liverpool ce ta fara cin ƙwallaye ta hannun Cody Gakpo a minti na 20, sannan Luis Diaz ya kara na biyu a minti ɗaya tsakani.
Daga baya ne Gunners ta zare ɗaya ta hannun Gabriel Martinelli, sannan Mikel Merino ya farke na biyu a karawar tsakanin ta ɗaya da ta biyun teburi.
Sai dai kuma minti bakwai tsakani Arsenal ta yi rashin Merino a fafatawar, sakamakon da aka yi masa jan kati a wasan na hamayya.
Wannan shi ne karo na biyu da suka tashi 2-2 a bana a Premier League, bayan karawar da suka yi a Emirates ranar 27 ga watan Oktoban 2024.
A wasan Gunners ta ci ƙwallaye ta hannun Bukayo Saka da Mikel Merino, ita kuwa Liverpool ta ci biyu ne ta hannun Virgil van Dijk da Mohamed Salah.
Tuni Liverpool ta lashe kofin Premier League na bana, kuma na 20 jimilla, irin yawan wanda Manchester United ta ɗauka a tarihin gasar.
Arsenal kuwa tana nan a mataki na biyun teburin Premier League da maki 68 da tazarar maki biyu tsakani da Newcastle United, wadda take ta ukun teburi.

Asalin hoton, Getty Images
A ranar ta Lahadi Virgil van Dijk ya buga wasa na 300 a Premier League, shi ne na uku ɗan kasar Netherlands da ya buga karawa da yawa a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Na farkonsu shi ne George Boateng da ya yi karawa 384, sai Denis Beckamp mai wasa 315 da kuma Van der Sar da ya buga fafatawa 313.
Liverpool ta yi wasa 16 a gida ba tare da rashin nasara ba kawo yanzu, tun bayan doke ta 1-0 da Nottingham Forest ta yi a Anfield ranar 14 ga watan Satumba.
Sauran wasannin da ke gaban Liverpool a Premier League:
Premier League ranar Litinin 19 ga watan Mayu
- Brighton da Liverpool
Premier League ranar Lahadi 25 ga watan Mayu
- Liverpool da Crystal Palace
Sauran karawar da ke gaban Arsenal a Premier League:
Premier League ranar Lahadi 18 ga watan Mayu
- Arsenal da Newcastle
Premier League ranar Lahadi 25 ga watan Mayu
- Southampton da Arsenal











